Wani Ya Roki Allah Ya Azurta Shugaba Jonathan da Mai Dakinsa da Karbar Musulunci

Wani Ya Roki Allah Ya Azurta Shugaba Jonathan da Mai Dakinsa da Karbar Musulunci

  • An ga abin mamaki a dandalin sada zumunta na Twitter biyo bayan abin da ya faru da Aminu Muhammad
  • Wani mai suna Romantic Guy ya nemi gafarar Allah kan cin mutuncin da ya yi wa Shugaba Goodluck Jonathan
  • Bayan neman yafiyar Ubangiji, Romantic Guy ya rokawa Jonathan da Uwargidarsa damar shiga Musulunci

Wani Bawan Allah a dandalin Twitter da ya bayyana kan shi a matsayin Romantic Guy, ya tuna da mulkin Shugaba Goodluck Jonathan.

Masu iya maganan Hausawa suna cewa duk wanda ya tuna bara, bai ji dadin bana ba. Da alama abin da ya faru da Sir Romantic Guy kenan.

Matashin ya yi amfani da shafinsa yana yabon Dr. Goodluck Jonathan da mai dakinsa, Patience Jonathan wadanda suka bar mulki a 2015.

Kamar yadda ya nuna, shi da wasunsa sun rika yin batanci ga Goodluck Jonathan, ya roki yafiyar Ubangiji, sannan ya roka masu musulunta.

Ana kewan Goodluck Jonathan?

Da alama wannan mutumi yana yin hannunka mai sanda ne ga magajin Jonathan, Muhammadu Buhari da kuma uwargidarsa, Aisha Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga abin da ya fada a shafinsa, mun kuma tattara wasu daga cikin martanin jama’a:

“Allah ka yafe mana cin mutunci da mu kayi musu.
Allah ya azurtasu da karbar musulunci.”

- Sir Romantic Guy

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan da Dame Patience Jonathan Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Mutane Wallahi kun raina Allah, a baya kun ce Allah ya la’ance shi, yanzu kuma kuna Allah ya masa albarka.

- Khalifa Qasim

Daman an ce so makaho ne, lokacin da muke cikin soyayya ba mu ji ba mu gani, mu ka ci masu mutunci, Wayyo! Allah Sarki!

- Muhammad Yakub

@Muhyakumar

Wai dama akwai irin wannan ranar tana zuwa? Allah mun tuba

- Mohammed Ladan

Shi kuwa wani yake cewa:

Wallahi kuwa, Ameen ya Rabb. Yanzu na gane kirkinsu. Allah ya yi maka albarka.

Khadija Sani tace:

“Mai wuya ne a maida kamarsa.”

Wani yace:

Kun ji wuta kenan. Ba rabo da gwani ba.

Aisha Buhari da Aminu Muhammad

An ji labari mutane irinsu Naja'atu Muhammadu suna sukar matar shugaban Najeriyan saboda tsare wani saurayi kan kalaman da ya yi a Twitter.

Tsakanin 2010 da 2015, an yi lokacin da mutanen kasar nan suka rika cin mutuncin Shugabansu, har mai dakinsa ba ta tsira ba, amma ba a kama su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel