An Tsinta Gawar ‘Yar Magajiya a Dakin Otal Bayan Gama Sharholiya da Kwastoma

An Tsinta Gawar ‘Yar Magajiya a Dakin Otal Bayan Gama Sharholiya da Kwastoma

  • Jami’an ‘ya sanda a garin Zaria dake jihar Kaduna sun gano gawar wata budurwa mai suna Blessing John a dakin wani otal dake Sabon Gari
  • Bayanan da aka tattaro a kai shi ne, ana zargin kwastomar ‘yar magajiyan ne ya halaka ta bayan kama dakin otal da suka yi tare don sharholiya
  • An gano cewa, budurwar ta zo daga jihar Binuwai ne makonni uku da suka gabata inda ta tsunduma harkar neman kudi da jikinta a Sabon Gari

Zaria, Kaduna - An tsinta gawar wata budurwa mai suna Blessing John a dakin wani otal dake Benin Street a Sabon Gari dake Zaria ta jihar Kaduna.

‘Yar Magajiya ta sheka lahira
An Tsinta Gawar ‘Yar Magajiya a Dakin Otal Bayan Gama Sharholiya da Kwastoma. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Otal din da ya kasance tamkar gidan magajiya, an gano ana kai mata marasa daraja domin sharholiya idan an kama shi.

Kara karanta wannan

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

Wani mutum dake zama kusa da otal din da ya bukaci a boye sunansa, yace:

“Ana zargin kwastoman budurwar ne ya halaka ta kwanaki biyu da suka gabata kafin a samu gawar wurin karfe 5:30 na yammacin Lahadi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Bayan shakar warin ne hankalin mutane ya kai dakin. An gayyaci ‘yan sanda kuma sun balle kofar tare da samun gawar. ‘Yan sanda sun dauka gawar tare da kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.”

Daga bisani an sake ganowa cewa budurwar ‘yar asalin jihar Binuwai ce wacce ta iso Zaria makonni uku da suka gabata inda ta fada harkar neman kudi da jikinta.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa, an kama manajan otal din kuma ‘yan sanda sun garkame shi domin bincike.

Duk kokarin da aka yi na samun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya faskara saboda wayarsa bata zuwa a yayin da aka rubuta wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Bada Umarnin Jefa IGP na Yan Sanda Gidan Yari

Legit.ng Hausa ta zanta da ganau

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da wani ganau dake da shagon siyar da jakunkuna a Benin Street dake Sabon Gari mai suna Malam Habu mai Takalmi, yace tabbas wari ya isa mutane na tsawon kwanaki amma ba a gane warin mene ne ba.

Bayan ‘yan sanda sun balle dakin otal din ne aka samu gawar Blessing wacce ta fara rubewa.

“Sanannen abu ne cewa matan da suka baro gidajen iyayensu ko suka gagara suna zuwa nan su kama dakuna inda suke zaman kansu.
”Hakan ce kuwa ta faru da Blessing amma ashe ba zata yi karko a harkar ba. A cewar abokan harkarta, makonni uku kenan da ta zo Sabon Gari kuma ajalinta yayi.
”Har a Yau dai ‘yan sanda basu sanar da abinda yayi ajalinta ba. Allah ya kare mu daga mutuwa irin wannan.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel