A Yau Talata Shugaba Muhammadu Buhari Zai Kaddammar Da Aikin Hako Fetir A Yankin Arewa Maso Gabas

A Yau Talata Shugaba Muhammadu Buhari Zai Kaddammar Da Aikin Hako Fetir A Yankin Arewa Maso Gabas

  • Yayin Da Buhari Zai Kaddamar Da Aikin Hakar Mai A Arewa, Mazauna yankin Sun Bukaci A Yi Musu Aiki, Da Tsaftataccen Muhalli
  • Shugabannin al’umma da mazauna jihohin Bauchi da Gombe sun yi kira da a samar da ayyukan yi da kuma taswirar tsaftar muhalli kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari.
  • Tun Kusan Shekarar 2019 dai ake ta fama dan ganin an gano tare da tuno danyen man fetir din a jihohin Gombe, Bauchi da Barno

Bauchi: Shugabannin al’umma da mazauna jihohin Bauchi da Gombe sun yi kira da a samar da guraben ayyukan yi da kuma tsarin tsaftar muhalli yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kaddamar da aikin hako mai na farko a Arewacin Najeriya a yau.

Sun bayyana wannan ci gaban a matsayin wata hanyar hasakaka a rayuwarsu. Amma a duk da haka sunyi kira ga shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa ba a mayar da al’ummarsu gefe ba ta fuskar daukar ma’aikata, yanke shawara, biyan diyya da sauran damammaki.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Bada Umarni a Karbe Miliyoyi da Gidajen Hadiman Sambo Dasuki Har Abada

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa "shiri yai nisa a kogin Kolmani da ke tsakanin Bauchi da Gombe inda shugaba Buhari zai jagoranci taron wanda ke da dimbin tarihi a arewancin kasar.

A garin Gombe, Jaridar Aminiya ta lura da yadda manyan jami’an kamfanin man fetur na kasa (NNPC) da kuma kamfanin ci gaban kasar New Nigerian Development Company (NNDC) suka yi tattaki zuwa wurin domin yin shirye-shiryen aikin hako mai na farko.

buhari
A Yau Talata Shugaba Muhammadu Buhari Zai Kaddammar Da Aikin Hako Fetir A Yankin Arewa Maso Gabas Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lasisi na neman mai lambar (OPL) 809 da 810 Kolmani na hannun NNDC ne, kamfani mai saka hannun jari na jahohin Arewa 19 tare da hadin gwiwar kamfanin NNPC da kuma wanda suke aikin kwangilar mai suna Production Sharing (PSC).

Yaushe Aka Fara Aikin

Kara karanta wannan

Alkawuran Atiku: Zan yiwa Arewa aiki kamar Abubakar Tafawa Balewa idan na gaji Buhari a 2023

Duk da cewa an fara binciken ne sama da shekaru 30 da suka gabata, an dakatar da shi saboda wasu dalilai amma a shekarar 2019, kamfanin na NNPC ya sanar da gano man a adadi mai yawa na kasuwanci a yankin kogin Kolmani.

A watan Satumba na 2021, ta fara haɓaka hakko rijiyoyin mai, wanda ya ƙunshi hako mai a matakin sama da aikin tsaka-tsaki na ganga 50,000 a kowace rana. matatar man dai zatai amfani da wutar lantarki megawatts 150 (MW).

An ga yadda jami’an tsaro yadda suka tsaurara tsaro a hanyar Gombe zuwa Bauchi har wajen da za'a gudanar da aikin a kauyan da suka hada da Garin Kafin Abbas da ke karamar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Mai Mutane Ke Cewa

Wani mazaunin garin Alkaleri, Malam Aliyu Adamu ya ce sun ji dadi.

“Babban abin da ke damun mu game da ayyukan shi ne lalacewar muhalli domin kashi 90 na mutanen Alkaleri manoma ne manoma wadanda suka dogara da noma da kiwo a matsayin hanyar rayuwa. Ba ma son yanayin da aikin hakar mai zai lalata mana muhalli da sakacin gwamnati kamar yadda ake gani a yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Gwmnati Tana Sa Ido da Kyau, EFCC Tana Bibiyar Kudin da ‘Yan Takara Suke Kashewa

“Kalubale na biyu da muke fargaba a kai shi ne batun samar da ayyukan yi ga matasan mu na hadin gwiwa domin kamfanonin da ke aiki a gidan man ba su dauki matasanmu aiki ba. Mun ga mutane daga wasu wurare suna gudanar da ayyukan " in ji Adamu.

A wata tattaunawa ta wayar tarho shugaban kungiyar matasa ta kasa (NYC) reshen Alkaleri, Kwamared Bala Mohammed Duguri, ya ce aikin hakar mai zai amfani jama’arsu domin zai bunkasa harkokin tattalin arziki.

"Muna fatan hakan zai haifar da kafa kanana da manyan kamfanoni domin kasancewarsu zai karfafa kasuwanninmu."

A Gombe ma wasu mazauna garin sun bayyana ra'ayoyinsu daban-daban dangane da gano lamarin. Malam Alhassan Yahaya yace Arewa ma ta iso.

“Mu ganin cewa an gano mai a yankin arewa maso gabashin kasar nan, labari ne mai dadi.
“Ya kamata gwamnati ta horar da ‘yan asalin jihar a fannin ilmin kasa, walda na masana’antu, injiniyoyin lantarki da sauran fannonin da za su yi amfani da su wajen samun damammaki a wuraren mai,” inji shi.

Kara karanta wannan

Jami’a ta Yaye Tsohon Ministan Buhari, Ya Kammala Digiri Bayan Komawa Gaban Malamai

A nasa bangaren, Shugaban kungiyoyi masu zaman kansu na Gombe (ANGOs) Kwamared Ibrahim Yusuf ya ce,

“Dole ne a lura da abubuwan da ke cikin gida ta bangaren ma’aikata da sauran abubuwan da za su tabbatar da cewa al’umma sun amfana. Aiwatar da dokar masana'antar man fetur zai taimaka sosai wajen kawar da tashin hankalin da ka iya tasowa daga hakko man."

Dr Musa Alkali, wani mazaunin garin ya ce bai kamata a maida batun siyasa ba.

“Muna cikin kakar siyasa, kasa da kwanaki 100 a gudanar da zabuka, ana yi wa jam’iyya mai mulki barazana, sai aka samu labarin hako mai a Arewa maso Gabas. Suna son ribatar mutane da haka.
“Duk da haka, idan da gaske sun gano man fetur din, ina ganin ci gaba ne mai kyau, zai kawo ci gaba a jihohinmu domin rabon da muke samu a kowane wata zai karu kuma zai ba gwamnatinmu kudade don ayyukan raya kasa,” inji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel