Abinda ka raina: Ana sayar da jakar 'Ghana-Must-Go' N860k a Amurka

Abinda ka raina: Ana sayar da jakar 'Ghana-Must-Go' N860k a Amurka

  • Wani sabon lamari da ya yadu a kafar sada zumunta ya ba mutane da dama mamakin gaske
  • An ga hoton jaka Ghana-Must-Go a wani shagon siyayya dauke da alamar farashi mai tsada
  • Mutane da dama sun yi martani, inda suka bayyana yadda suka ji da ganin yadda aka daraja jakar

Hoton mashahuriyar jakar nan da matafiya ke saye don shake ta da kaya wato 'Ghana must go' ya bazu a yanar gizo inda jama'a ke martani kan yadda aka bayyana darajar kudi na jakar.

Lamarin ya girgiza jama'a da dama a kafar sada zumunta lokacin da aka ga an makalawa jakar farashi $2090 (N860,390.30) a wani shagon sayayya na yanar gizon mai Balenciaga na kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

Abinda ka raina: Yadda ake sayar da jakar 'Ghana-Must-Go' N860k a Amurka
Ghana Must Go mai daraja | Hoto: @kennytrip2
Asali: UGC

Legit.ng ta leko wannan rubutun da wani mai suna @kennytrip2 ya wallafa a shafin sada zumunta tare da taken;

"Dakata .. meye? Shin ya kamata mu gaya musu?"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin da jama'a suka yi ya ba da dariya

Yayin da aka yi rubutun, mutane sama da dubu sun yi martani, inda kowa yake bayyana ra'ayinsa. Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin maganganun da ake fada.

@VoysZA ya ce:

"Dole Ghana ta zauna, tafiya tayi tsada."

Daga @jacksparo212:

"Yi tunani bayan siyan wannan jakar ka tafi kauye don nuna burga da ita.. Hehehe. Mutanen kauyen sai sun fashe da kuka."

@its_emeraldfx yayi sharhi kan maganar @jacksparo212:

"Za su ga zama kamar ba Ghana-Must-Go bane, mutanen kauye."

@l_a4shizzle ya ce:

“Yanzu za mu hanzarta siyansa saboda ba ma sayen abubuwa masu arha amma muna son siyan abubuwa masu tsada wadanda aka sace mana aka sake dawo mana dasu.

Kara karanta wannan

Da dumi: Kotu ta soke dakatarwar da aka yi min a matsayin Shugaban APC, Oshiomhole ya bayyana mataki na gaba

"Watakila ma su iya amfani da shahararriyar 'yar kasar Ghana a matsayin jakadiya kamar yadda aka nada Tiffany ya yi @Beyonce amb. na dutsen mai daraja na jini da suka sace daga Afirka..."

Garabasa: Matashi na neman budurwar da zata so shi, zai ba ta albashin N150k duk wata

A wani labarin mai ban al'jabi, wani matashi dan Najeriya wanda aka bayyana da suna Chudy mai amfani da suna @OkparaNnaJiAku a kafar sada zumunta ya ce yana neman budurwa wacce za ta fahimceshi ta yadda zai ke ba ta N150,000 a matsayin albashin wata-wata.

Chudy ya kuma nuna cewa adadin kudin zai rinka karuwa bayan watanni uku kuma zai ba da wasu karin garabasa da fa'idojin da suka hada da karin wata na 13, fansho, da sauransu.

Saurayin, wanda bayanansa suka nuna shi dan gwagwarmayar yanar gizo ne wanda ya ci lambar yabo, manazarcin bayanai, fasaha, masanin kudaden crypto da sauransu, ya ce duk mace mai sha'awar yin abin da ya bukata, kawai ta nuna alama.

Kara karanta wannan

Garabasa: Matashi na neman budurwar da zata so shi, zai ba ta albashin N150k duk wata

Maganarsa ta haifar da dimbin martani daga mutane sama da dubu biyu a lokacin da ya wallafa rubutun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel