Nayi babban kuskure: Bidiyo Ya Nuna Osinbajo Ya Nemi Afuwar Mai gidansa, Tinubu

Nayi babban kuskure: Bidiyo Ya Nuna Osinbajo Ya Nemi Afuwar Mai gidansa, Tinubu

  • A ranar Asabar aka ji Yemi Osinbajo ya na ba ‘Dan takaran APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu hakuri
  • Farfesa Osinbajo ya bada hakuri ne a dalilin mantawa da ya yi bai ambaci sunansa wajen jana’iza ba
  • Da aka ankarar da mataimakin shugaban kasar, sai ya amsa kuskurensa, ya yi maza-maza ya bada hakuri

Ondo - A ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamba 2022, aka ji Yemi Osinbajo ya manta da sunan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a wajen taron jana’iza a Ondo.

Shugabanni da manyan kasa sun halarci jana’izar mahaifiyar Gwamna Rotimi Akeredolu. The Cable tace Bola Tinubu yana cikin baki wajen taron.

An yi wa marigayiyar addu’a ne a cocin St. Andrew’s Anglican Church da ke garin Owo a Ondo. Rahotanni sun ce an bar majami'ar kowa yana fara'a.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Osinbajo ya ambaci sunayen manyan ‘yan siyasa, fitattun mutane, ‘yan jam’iyyarsa da na adawa, tsofaffin gwamnoni, ‘yan majalisa da kuma ‘yan kasuwa.

Osinbajo bai lura da Tinubu ba

Amma da ya tashi jero wadanda suke wurin makokin, mataimakin shugaban kasar bai ambaci sunan tsohon mai gidansa watau Asiwaju Bola Tinubu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai da wani hadiminsa ya ankarar da shi tukuna, ya dauki takarda ya sanar da shi cewa Bola Tinubu yana sahun farko a gabansa, sannan Farfesan ya lura.

Grace Akeredolu
Jana'izar Grace Akeredolu Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC
“Kafin in cigaba, nayi babban kuskure. Na manta da ‘dan takaran kujerar shugaban kasa a babbar jam’iyyar mu ta APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Emilokan. Asiwaju, tuba nake yi. Yana zaune nan a kusa da ni. Ba a kusa da ni kawai ba, ga shi nan a gaba, ina maka maraba da zuwa taron nan.”

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Alkawarin Karasa Aikin da Aka Yi Shekara 43 An Gaza Kammalawa a Arewa

Osinbajo ya kira sunayen irinsu tsohon Gwamnan Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, sai Gwamnonin jihohin Legas da Ogun; Babajide Sanwo-Olu da Dapo Abiodun.

An yi maganin jita-jita

Wannan abin da hadimin ya yi, zai taimaka wajen kore rade-radin rashin jituwa tsakanin tsohon gwamnan na Legas da Kwamishinansa a lokacin yana ofis.

Osinbajo ya nemi tikitin zama ‘dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC a 2023 tare da Bola Tinubu. A karshe mataimakin shugaban Najeriyan ya sha kashi.

APC za ta sake zabe a Taraba

A ranar Litinin aka ji labari Alkali yace zaben da APC ta shirya wanda ya ba Sanata Emmanuel Bwacha damar zama ‘dan takarar Gwamna a Taraba ya saba doka.

Kotun tarayya na Abuja tayi umarni ga jam’iyyar APC tayi maza ta sake gudanar da zaben ‘dan takaran da zai rike mata tutar zama Gwamnan jihar Taraba a 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban EFCC Ya Ga Tinubu a Aso Rock, Ya Ambaci Abin da Zai Taimaki APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel