Magana ta dawo baya: Ba Mu Yanke Ranar Dawo da Jirgin Kaduna-Abuja ba – NRC

Magana ta dawo baya: Ba Mu Yanke Ranar Dawo da Jirgin Kaduna-Abuja ba – NRC

  • Hukumar NRC ta yi karin bayani a game da shirye-shiryen dawo da jiragen kasan Kaduna zuwa Abuja
  • Shugaban hukumar kula da harkokin jirgin kasa yace ba a tsaida ranar da za a dawo bakin aiki ba tukun
  • Fidet Okhiria yace ana kokarin ganin kafin wata mai-ci ya shude jiragen sun koma daukar fasinjoji

Abuja - Hukumar NRC mai kula da harkokin jirgin kasa, ya karyata jita-jitar da wasu gidajen yada labarai da kafafen sada zumunta suke yadawa.

Shugaban hukumar NRC na kasa, Fidet Okhiria ya fadawa hukumar dillacin labarai watau NAN cewa ba su sa ranar da jirage za su koma aiki ba.

Ana yada labari da bai tabbata ba cewa a watan Nuwamban nan jiragen kasan Kaduna zuwa Abuja za su cigaba da aiki kamar yadda suka saba.

Kara karanta wannan

Idan ya gaji Buhari: Kwankwaso ya magantu kan ko zai ke tafiya kasar waje neman magani

Daily Trust ta rahoto Fidet Okhiria a ranar Lahadin nan, yana cewa wannan batu ba gaskiya ba ne.

Babban Darektan na hukumar NRC ya yi kira ga jama’a da suyi watsi da maganar, yace har yanzu gwamnati ba ta kai ga tsaida lokacin dawowa ba.

Muna kokarin ganin hakan - NRC

Amma a tattaunawar da ya yi da ‘yan jarida, Okhiria ya tabbatar da cewa ana kokarin ganin jiragen sun dawo daukar fasinjoji kafin karshen Nuwamba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jirgin kasa
Jirgin kasa a Najeriya Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

“Ina so in sanar da daukacin jama’a cewa labarin ba gaskiya ba ne, saboda ba a tsaida rana ba tukuna.
Da gaske ne Minista ya bada sanarwar za mu koma bin hanya a Nuwamban nan, kuma ana kokarin ganin mun dawo bakin aiki kafin karshen Nuwamba.
Ina mai kara tabbatar da kokarin gwamnatin tarayya da hukumar wajen kare lafiya da dukiyoyin fasinjojinmu masu daraja da kuma mutanen Najeriya.-

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Akwai Kudi Dankam a Najeriya, Ba Zamu yi Rance Don Biyan Albashi ba

- Fidet Okhiria

Watani 8 jirgin kasan ba ya aiki

Jaridar nan ta Premium Times ta fitar da rahoto, tace babu tabbacin jiragen kasan na Kaduna-Abuja su cigaba da jigilar fasinja nan da 24 ga watan nan.

Zuwa yanzu jirgin ya yi watanni takwas ba tare da ya yi aiki ba a sakamakon harin da ‘yan ta’adda suka kai, har suka yi garkuwa da wasu matafiya.

Na san a rina - Amaechi

A lokacin da 'yan ta'adda suka kai harin, Rotimi Amaechi yana kujerar Ministan sufuri na kasa, an ji labari yace ya yi hasashen hakan za ta faru.

Hon. Rotimi Amaechi ya ce tun farko sai da ya bukaci a kashe N3bn wajen sayan wasu kayan tsaro, amma gwamnatin tarayya ba ta saurare shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel