Wani Mahaifi Ya Zuba Wa Diyarsa Guba a Shayi Saboda Ta Fara Soyayya

Wani Mahaifi Ya Zuba Wa Diyarsa Guba a Shayi Saboda Ta Fara Soyayya

  • Wani mutuni magidanci, Mista Chuks Johnson, ya zuba wa 'yarsa da ya haifa guba a shayi a Kubwa da ke birnin tarayya Abuja
  • Mahaifiyar matashiyar budurwar tace Mijinta na kokari ta kowane fanni don ta yi karatu amma kawai ta fara soyayya da wani
  • Tace sai da aka shafe awanni kafin Likitoci su yi nasarar ceto rayuwarta, tuni aka kai rahoto ga hukumar yan sanda

Abuja - Wani magidanci mai suna, Chuks Johnson, a Kubwa da ke yankin ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja ya yi yunƙurin kashe ɗiyarsa ta cikinsa.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Mutumin ya yi kokarin halaka ɗiyarsa ne ta hanyar gauraya maganin Kwari da Shayinta ranar Litinin da Safe.

Shan guba a abin sha.
Wani Mahaifi Ya Zuba Wa Diyarsa Guba a Shayi Saboda Ta Fara Soyayya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Lamarin, a cewar jaridar City & Crime, ya auku ne a Arba Road dake garin kuma mahaifiyar yarinyar ta tabbatar da haka ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ASUU ta magantu kan za ta fara sabon yajin aiki ko kuma za ta ci gaba da aiki

A wata tattaunawa, Mahaifiyar matashiyar budurwar, Misis Ruth Chuks, ta faɗa wa wakilin jaridar cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ɗiyata ta kulla soyayya da wani ɗan saurayi dake zaune a garinmu, a baya yayarta ta gudu ta bi saurayinta zuwa Kaduna. Yanzu kuma ƙaramar, wacce ke neman Admission ɗin shiga babbar makaranta, ta fara soyayya."
"Mahaifinta bai gaza mata ta kowane fanni ba, komai ta bukata yana samar mata. Ya gargaɗeta ta rabu da Saurayin amma ta yi kunnen ƙashi, hakan ya sa ya zuba mata maganin Kwari a Shayi."
"Na ga lokacin da ya siyo gubar amma bansan niyyarsa ba. Tana shan cokali ɗaya na Shayin ta fara canzawa. Na roke shi ya taimaka mana da Motarsa mu kaita Asibiti, haka muka garzaya Asibiti ba tare da maƙotanmu sun san komai ba."

Shin yarinyar ta farfaɗo?

Ya ƙara da cewa sai da Likitoci a Asibitin suka shafe awanni da dama kafin Allah ya taimaka yarinyar ta iya farfaɗowa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Buhari Ta Sanar da Lokacin Cigaba da Sufurin Jirgin Kasa a Titin Kaduna-Abuja

Misis Ruth tace a halin yanzun sun kai rahoton abinda ya auku ga hukumar 'yan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace.

A wani labarin kuma wani Magidanci Ya Nemi Kotu ta Raba Aurensa da uwar 'yayansa, ya faɗi yadda ya ganta tana saduwa da ɗan uwansa

Justine Onu, ɗan kasuwa mazaunin birnin Tarayya Abuja ya garzaya Kotu yana neman raba aurensa domin ya gaji da matar da ta sa masa hawan jini.

Da yake labartawa Kotun munanan halayen mai ɗakinsa, Magidancin yace a duk lokacin data haɗu da mutum burinta kawai ta kwanta da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel