Za a Fara Biyan Albashin Watanni 8 ga 'Yan CONUA da Suka Fita daga ASUU

Za a Fara Biyan Albashin Watanni 8 ga 'Yan CONUA da Suka Fita daga ASUU

  • Ana sa ran cewa daga yau Gwamnatin tarayya za ta fara biyan albashi malaman jami’a da aka rike
  • Albashin watanni takwas da za a biya ba zai shafi ‘yan kungiyar ASUU da suka shiga yajin-aiki ba
  • Alamu na nuna za a biya tulin kudin ne ga ‘Ya ‘yan kungiyar CONUA da suka bangare daga ASUU

Abuja - Gwamnatin tarayya za ta soma biyan bashin albashin watanni takwas da suka taru ga malaman jami’an da suka yi yajin-aiki a shekarar nan.

Daily Trust a rahoton da ta fitar a yammacin Lahadi, 6 ga watan Nuwamba 2022, tace ‘yan kungiyar nan ta CONUA ne kurum aka ware za a biya kudin.

Kungiyar CONUA ta bangare ne daga ASUU, wanda ta jagoranci dogon yajin-aikin da aka yi. Punch ta rahoto cewa akwai yiwuwar gwamnati ta fito da kudin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daga Karshe, Ngige ya bayyana dalilin biyan Malaman Jami'a rabin albashi

Wani ‘dan kungiyar CONUA da ke karantarwa a jami’ar Obafemi Awolowo a Ile Ife, ya shaidawa jaridar cewa Chris Ngige ya nuna zai biya su kudin da suke bi.

"Yau za a fara biyan mu"

Malamin jami’ar yake fada a ranar Lahadin nan cewa Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, ya kyankasa masu cewa za a biya su albashinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wannan malami da ya yi hira da manema labarai ba tare da ya bari an dauki sunansa ba, Minista ya fada masu su sa ran shigowar kudinsu a yau.

Chris Ngige
Sanata Chris Ngige Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Majiyar ta shaida cewa Ministan ya yi alkawari zai magance matsalar rabin albashin da aka biya malaman jami'a, amma wannan ba zai shafi ‘Ya 'yan ASUU ba.

"Ba mu cikin yajin-aikin karshe da aka yi. A baya mun rubutawa ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi. Saboda haka Minista ya duba, ya dauki mataki."

Kara karanta wannan

Tsaiko ga daliban Najeriya yayin da ASUU ke shirin komawa yajin aiki saboda dalili 1

- Malamin jami'ar

An yi yunkurin a tuntubi shugaban CONUA na kasa, Niyi Sunmonu, amma ba a samu wayarsa ba.

Za a biya wadanda ba su yi yajin-aiki ba

Mai magana da yawun Ministan tarayyar, Olajide Oshundun ya tabbatarwa manema labarai cewa za a biya ‘yan CONUA muddin ba su shiga yajin-aiki ba.

Olajide Oshundun yace gwamnatin tarayya ba za ta biya sauran malaman jami’a ba, saboda akwai dokar da tace babu albashi ga wanda bai yi aikinsa ba.

ASUU na shirin zama

Mun fahimci cewa gwamnatin tarayya ta dauki wannan mataki ne a lokacin da aka ji labari shugabannin ASUU su a shirin yin zaman majalisar koli ta NEC.

Farfesa Emmanuel Osodele ya tabbatar da cewa Kungiyar ASUU za tayi taro a dalilin biyan malaman jami’a rabin albashinsu da aka yi a Oktoban da ta wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel