Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

  • Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa idanun hukumar na sanye kan wasu gwamnoni 3 dake son biyan albashin ma’aikatansu da tsabar kudi a maimakon ta banki
  • Bawa ya bayyana cewa, ana zargin gwamnonin da ajiye tsabar kudaden a gidajensu wanda kuma yanzu basu san yadda zasu yi dasu ba saboda sauya kudin kasar nan da za a yi
  • Yace ba zasu hakura da kai samame wurin ‘yan canji ba kuma idanunsu na sanye kan dillalai da ake tururuwar siyan kadarori saboda a batar da makuden kudaden da ba na halas ba

FCT, Abuja - An sanyawa gwamnoni uku dake kan karagar mulki ido kan yadda zasu yi da makuden biliyoyin da suka boye kuma suke don biyan albashin ma’aikata da su, shugaban Hukumar yaki da rashawa, Abdulrasheed Bawa ya sanar da Daily Trust a zantawar da suka yi ta musamman a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji

Bawa da Buhari
Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC. Hoto daga Presidency
Asali: Facebook

Yace samamen da suke kaiwa ‘yan canji zasu cigaba inda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayansu domin amfanin kowa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust ta rahoto cewa, babban bankin Najeriya a ranar 26 ga watan Oktoban 2022 ya sanar da cewa kasar nan zata canza wasu takardun kudadenta domin dakile matsalolin tattalin arziki da suka addabeta.

Yayin da za a saki sabbin kudaden a ranar 15 ga watan Disamba, ‘yan Najeriya suna da har zuwa ranar 31 ga watan Janairun shekara mai zuwa don su kai tsofaffin kudaden banki.

Sai dai kokarin da manyan ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, masu zuba hannayen jari da sauran jama’a ke yi na canza Naira zuwa daloli ya fara kawo matsala ga tattalin arzikin kasar.

Gwamnoni 3 EFCC ta zubawa idanu

Kara karanta wannan

“Naki Sanarwa Matata da ‘Da na”, Magidancin da Yaci N13bn a Caca

A hirar da Daily Trust tayi da Bawa, ya bayyana cewa wasu gwamnonin suna kokarin ganin sun killace kudaden da suka sata. Yace a Yanzu haka suna kallon uku daga ciki.

Bawa wanda ya ki bayymana sunayen gwamnonin uku, yace biyu daga cikinsu na arewa ne yayin da dayan yake daga kudancin kasar nan.

Yace bayanan sirri da hukumar ta samu sun bayyana cewa gwamnonin sun kammala shirin zuba kudin ta hanyar biyan albashi da tsabar kudin wanda zasu ba ma’aikata a hannu.

“Bari in fada muku wani abu, kuma ina son ku dauka wannan abun da muhimmanci. Tuni wasu gwamnonin da suka dankara kudi a gidajensu tsabarsa suke kokarin biyan albashi da su a jihohinsu.”

Da aka tambayesa ko hukumar zata kira gwamnonin, shugaban EFCC yace suna dai sanye da idanu a kansu.

Ya kara da cewa:

“Ban san yadda suke don su yi hakan ba, amma dole ne mu hana su. Muna dai aiki a kai, ba su riga da sun biya albashin ba da tsabar kudin amma abu ne mai girma.”

Kara karanta wannan

Miyagun ‘yan Bindiga Sun Harbe ‘Yan Sanda 3, Sun Sace Hamshakin mai Arziki

Yace hakan ya ci karo da sashi na biyu na kundin hana wanke kudin sata su koma kamar na halal.

“Dokar a bayyane take kan hada-hadar tsabar kudi. Duk wanda zai yi wata hada-hadar tsabar kudi a matsayinsa na shi kadai kada ya zarce N5 miliyan, sai na kamfani kuma kada ya wuce N10 miliyan.
“Tabbas na yarda albashin basu kai hakan ba amma saboda mene kwatsam ana biyan albashi ta banki kuma yanzu zaku biya da tsabar kudi, me ku ke kokarin yi? Zasu yi kokarin biya hakan shiyasa zasu tantance jami’ai, abinda muka samo kenan.”

- Yace.

Batar da boyayyun tsabar kudi ta hanyar siyan kadara

Shugaban EFCC ya tabbatar da cewa tururuwar da wasu jama’a ke yi na batar da tsabar kudin da suka boye suna yi ne ta hanyar siyan kadarori.

“Muna sane da hakan. Ko wadanda ke son batar da kudin ta hanyar siyan kadarori ne kuwa, kuna karbar kudin banki zasu nufa kafin ranar 31 ga watan Janairun 2023. Toh me zai faru, za ku zo banki da miliyoyin ko? Saboda haka ne muke aiki tare da ma’aikatan bankuna kuma idan kuna da bayanai ku turo mana.”

Kara karanta wannan

Bayan Sauyin Launi, Buhari Ya Nuna Inda Sababbin Kudin da Aka Yi Suka Bambanta

- Yace.

Za a cigaba da kai samame wurin ‘yan canji

Yace za a cigaba da kai samame wurin ‘yan canji. Hakan yace yana da matukar amfani wurin hana fito da kudin sata.

“‘Yan canji suna da matukar amfani a wannan bangaren saboda mutane da yawa dake da naira zasu so mayar dasu daloli ko kudin kasashen waje.”

Dalilin da yasa na gana da jami’an bankuna

A kan dalilin da yasa Bawa ya gana da manyan jami’an bankuna a Legas baya-bayan nan, yace duk hakan na cikin kokarin sanyawa tsarin ido tare da neman hadin kansu a bangaren yuwuwar kawo kudin haram bankunan.

“Mun san cewa mutane da yawa suna ajiye da kudi, suna tare da su kuma zasu samu hanyar mayar dasu bankuna.
“Toh ba tare da duban abinda suka yi da tsabar kudin ba, ko kuma su yi musaya da daloli, ko su yi amfani da shi wurin siyan gidaje, duka ta kowacce hanya dai sun dawo bankunan.

Kara karanta wannan

Bayan Buhari Ya Kaddamar, 'Yan Najeriya Sun Maida Martani Game da Sabon Sumfurin Kudin Naira

“Toh ba tare da duban abinda aka yi da kudin ba, bankuna suna da matukar amfani saboda su ne dai zasu karba kudaden tsabarsu.
“‘Yan canji dole bankuna suke zuwa su zuba kudin kafin su samu kudaden ketare, dillalan gidaje ma haka suke yi. A don haka ne muka zauna da su tare da yin yarjejeniya kan abinda ya dace su yi. Kowa na farin ciki da hakan.”

- Yace.

Kada ku tsorata

Sai dai Bawa yayi kira ga ‘yan Najeriya da cewa kada hankulansu ya tashi saboda sauya kudi, dama babban bankin ya saba kuma aikinsa ne wanda ya dace a dinga yi kowacce shekaru takwas domin kudi su koma musu.

“Abinda gwamnati ke cewa shine ku kai kudaden ku bankunan, babu kudin da za a caje ku, shikenan.
“Ta yaya tattalin arziki zai inganta bayan kashi 80 na kudin kasa suna waje kuma wasu ne suka boye su?.”

- Bawa ya kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel