Wuta Ta Kama a Babban Kantin Yan Sanda a Nasarawa, Ta Lakume Miliyoyin Naira

Wuta Ta Kama a Babban Kantin Yan Sanda a Nasarawa, Ta Lakume Miliyoyin Naira

  • Wata wuta ta lakume dukiyar miliyoyin Naira a rukunin shagunan Plaza ta yan sanda da ke Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa
  • Bayanai sun nuna cewa Wutar ta kama ne sakamakon tartsatsin Wutar lantarki tun karfe 1:00 na dare har karfe 7:00 na safe
  • Wani ganau yace jami'an kashe wuta sun zo a kan lokaci amma ba su iya daƙile wutar ba sai da safiya bayan wasu sun kawo musu ɗauki

Nasarawa - An tafka asarar dukiya ta miliyoyin naira bayan wata Gobara ta ɓarke a rukunin kantuna POWA Plaza, dake kan Titin Jos, a Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Ganau ya shaida wa wakilin jaridar Punch cewa Wutar ta tashi ne daga wutar lantarki a ɗaya daga cikin shagunan da ke Plazar da misalin ƙarfe 1:00 na dare wayewar garin Talata.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar PDP Ta Sanar da Sakamakon Zaɓen Fidda Gwanin da Ta Canza a Kaduna

Taswirar jihar Nasarawa.
Wuta Ta Kama a Babban Kantin Yan Sanda a Nasarawa, Ta Lakume Miliyoyin Naira Hoto: punchng
Asali: UGC

Yace wutar ta kone mafi yawan dukiyar da ke rukunin shagunan mallakin rundunar yan sanda kafin daga bisani jami'an kwana-kwana su samu nasarar kashe wutar.

Vanguard ta rahoto mutumin na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wutar ta fara ci ne wajen ƙarfe 1:00 na dare wayewar garin Talata, ta cinye dukiyoyi na Miliyoyin Naira kafin zuwan jami'an kashe gobara. Duk da haka ba su iya dakile wutar ba har sai karfe 7:00 na safe lokacin da aka ƙaro jami'ai."
"Shaguna sama da Bakwai wutar ta babbake, shagon ɗinki, shagon sayar da sabbin tufafin zamani, Shagon Sola da wasu manyan Shagunan kasuwanci sun kone ƙurmus."
"Ina tausayawa masu kasuwancin ta yadda zasu iya jure wa bayan wannan Asara mai girma da Allah ya jarabcesu. Gaskiya ya kamata gwamnati ta duba yuwuwar tallafa musu."

Legit.ng Hausa ta gano cewa POWA Plaza na gefen Ofishin kwamandan yanki na rundunar 'yan sandan Lafiya kuma tana kallon kallo da Ofishin yakin neman zaɓen Gwamna Abdullahi Sule.

Kara karanta wannan

NDLEA: Yadda muka yi ram da makaho ‘Dan kasar waje dauke da miyagun kwayoyi

An rasa rayuka a wata Gobara a makarantra Tsangaya a Kano

A wani labarin kuma Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Dakin Kwanan Dalibai a Makarantar Tsangaya a Jihar Kano

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wata makarantar Tsangaya a jihar Kano, kamar yadda hukumar agaji ta tabbatar.

Akalla dakuna 14 ne suka kone kurmus, NEMA ta ba da tallafi mai yawa ga daliban makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel