Shekaru 3 Bayan Kammala Aikin Tashar Wutar Lantarki Ta Dadin-Kowa Mai Karfin Megawatt 40, Har Yanzu Ba Ta Aiki

Shekaru 3 Bayan Kammala Aikin Tashar Wutar Lantarki Ta Dadin-Kowa Mai Karfin Megawatt 40, Har Yanzu Ba Ta Aiki

  • Mutanen garin Dadin-Kowa a karamar hukumar Yamaltu/Deba Local na jihar Gombe sun koka kan jinkirin kaddamar da tashar lantarki na garin mai karfin megawatt 40
  • An kaddamar da aikin ne tun a shekarar 1988, lokacin mulkin shugaban soja Janar Ibrahim Babangida kuma dan kwangilar ya ce ya kammala a 2019
  • An yi shirin kaddamar da tashar lantarkin a sai dai an yi jinkiri saboda annobar korona a 2020 amma shekaru 3 bayan annobar ta yi sauki har yanzu ba a kaddamar ba
  • Mutanen garin Dadin-Kowa sun yi kira ga gwamnatin tarayya da wadanda abin ya shafa suyi bincike tare da gaggauta kaddamar da aikin don a fara amfana da shi

Gombe - A ranar 7 ga watan Nuwamba, za a cika shekaru uku tun lokacin da dan kwangilar da ke kula da aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatts 40 na Dadin-Kowa a karamar hukumar Yamaltu/Deba da ke jihar Gombe ya sanar da cewa ya kammala aikin.

Kara karanta wannan

An Ci Karo da Matsaloli, Gwamnatin Buhari Za ta Iya Shirya Sabon Kundin Kasafin kudi

Bayan shekaru uku, Daily Trust Saturday ta ziyarci tashan lantarkin ta kuma kawo rahoto kan yanayin rashin kula da cire rai da mutanen yankin suka yi.

Dadin-Kowa
Shekaru 3 Bayan Kammala Aikin, Tashar Wutar Lantarki Ta Dadin-Kowa Mai Karfin 40 MW Ba Ta Aiki. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

An fara aikin tashar lantarkin na Dadin-Kowa ne a 1959 kuma yana wurin da a yanzu ya fado jihar Gombe ne don samar da wuta megawatts 40.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutanen Dadin-Kowa da kewaye sun yi murna kan aikin wutan lantarkin da cigaba na tattalin arziki da zai kawo jiharsa, arewa da kasa baki daya.

Tun kafin Najeriya ta samu yanci aka fara aikin tashar lantarki na Dadin-Kowa

Duk da cewa an fara aikin ne shekara guda kafin Najeriya ta samu ’yancin Najeriya, ba a bada kwangilar gina madatsar ruwa ba sai 1980, sannan aka kaddamar da aikin bayan shekaru takwas, a 1988, karkashin shugaban mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Kara karanta wannan

Gwamnati zata tallafawa yan kasa wajen rage tsadar kayyayyakin ainci, Ministan Noma

Tafkin yana iya rike ruwa mita cubic miliyan 800 da fadin kasa kilomita 300.

Dam din na iya samar da kifi, amma ba a yi wani abu mai mahimmanci ba game da damar samar da wutar lantarki ba sai kwanan nan, rahoton Daily Trust.

Duk da yake an kaddamar da dam kusan shekaru 34 da suka shude, wanda aka tsara don samar da 40MW na lantarki, aiki a bangaren lantarki ya rika gaba da baya bayan kammala dam din.

Dam din Dadin-Kowa yana kilomita 5 daga arewacin kauyen Dadin-Kowa da kuma kilomita 37 daga garin Gombe, a kan hanyar Biu.

Ana fatan zai janyo kanana da matsakaita da manyan kamfanoni zuwa yankin, wanda zai samar da ayyuka ga dubban matasa da samar da kudin shiga ga jihar.

Mai kula da kwangilar tashar Dakin-Kowa ya ce aikin ya kammala tun a 2019

Shugaban MABON Energy Limited, mai kula da kwangilar, Mr Cyril Christopher, a ranar 7 ga watan Nuwamba ya sanar da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya yayin ziyarar ban girma, ya ce aikin na biliyoyin naira ya kammala kuma jira ake yi a kaddamar.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

Domin amfana da wutar lantarkin, gwamnatin jihar Gombe ta ware hekta 1,000 da ke kusa da Dadin-Kowa domin gina wani wurin shakatawa da aka sala wa suna ‘Muhammadu Buhari Industrial Park'.

Sai dai, farin cikin mutane da suka dade suna jira a kammal a aikin tsawon shekaru bai dade ba saboda bayan shekaru uku da kammalawar, ba a kaddamar ba.

An jinkirta kaddamarwar da aka shirya Shugaba Muhammadu Buhari zai yi saboda annobar COVID-19.

Amma shekaru biyu bayan an ci karfin annobar, har yanzu ba a kaddamar da aikin ba kuma babu bayani dalilin hakan daga FG ko dan kwangilar da ke kula da aikin.

Mazauna Dadin-Kowa sun yi korafi

Saboda rashin kaddamawar, mazauna Dadin-Kowa, garin da aka gina tashar samar da wutar lantarki, sun nuna rashin jin dadinsu kan jinkirin da aka samu wajen kaddamar da aikin, shekaru uku da kammala aikin.

Wani mazaunin garin, Musa Ibrahim, ya ce basu ji dadi ba yadda mahukunta suka gaza cika alkawarin kaddamar da aikin bayan kammala shi, da shekaru suna jira.

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Mai unguwa, wanda ke sana'ar sayar da kankara ya koka kan rashin wadataccen wutar lantarki a garin.

Ya ce:

"Muna fama da kallubale, da an kaddamar da tashar lantakin, da an samu cigaba a garin kuma mutane ba za su wahala ba.
"Da an bude kamfanoni a nan, wanda zai samarwa matasan mu ayyuka. Rai na ya baci sosai saboda jinkirin."

Wasu mazauna garin Dadin-Kowa sun ce suna shafe makonni babu wutan lantarki a gidajensu.

Masu sana'a irin aski, teloli, masu walda, da kankara da wasu da sana'arsu ta dogara ga lantarki sun koka kan jinkirin kaddamar da aikin saboda kudin da suke kashewa kan janareta.

Sun yi kira ga gwamnatin tarayya da wasu hukumomin da abin ya shafa su bincika halin da ake ciki su gaggauta kadamarwar.

Shugaba Buhari ya kama hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

Yayin da matsalar karancin wutar lantarki a Najeriya ke cigaba da ci ma jama’a tuwo a kwarya, shi kuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari matakin shawo kan matsalar gaba daya ya dauka bayan wata ganawa da yayi da masu rike da kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, kuma babban hadimin shugaba Buhari, Abba Kyari ne ya wakilci Buhari a yayin wannan zaman tattaunawa da kamfanonin, inda aka duba matsalolin dake janyo matsalar wuta, tare da duba hanyoyin magancesu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel