Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kama hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kama hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

Yayin da matsalar karancin wutar lantarki a Najeriya ke cigaba da ci ma jama’a tuwo a kwarya, shi kuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari matakin shawo kan matsalar gaba daya ya dauka bayan wata ganawa da yayi da masu rike da kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, kuma babban hadimin shugaba Buhari, Abba Kyari ne ya wakilci Buhari a yayin wannan zaman tattaunawa da kamfanonin, inda aka duba matsalolin dake janyo matsalar wuta, tare da duba hanyoyin magancesu.

KU KARANTA: Duka biyu: Gobara ta cinye kayan tallafin yan gudun hijira a jahar Borno

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kama hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya

Buhari ya kama hanyar shawo kan matsalar wutar lantarki a Najeriya
Source: Facebook

A makon data gabata, kafin shugaba Buhari ya amshi rantsuwa karo na biyu ne Abba Kyari ya gana da kamfanonin a fadar shugaban kasa, taron daya samu halartar ministan wutar lantarki, hukumar sayar da kadarorin gwamnati, da kuma hukumar cinikin wutar lantarki ta kasa.

A yayin zaman, kamfanonin sun bayyana matsalolin da suke fuskanta da suka hada da karancin iskar gas, karancin hanyoyin isar da wutar lantarki ga jama’a, karancin mitocin wutar lantarki, satar wutar lantarki da kuma yawan samun asara ta fuskar kasuwancin wutar, amma Kyari ya shaida musu cewa gwamnatin kasar Jamus zata agaza ma Najeriya akan lamarin.

A zamanin tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ne aka sayar da kamfanin wutar lantarki PHCN zuwa ga yan kasuwa, inda aka fasata zuwa kamfanonin samar da wutar lantarki guda 6, da kamfanonin rarraba wutar lantarki 11, amma har yanzu bata sauya zani ba.

Guda daga cikin mahalarta taron ya bayyana cewa “Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya gana da kamfanonin dake rarraba wuta, kuma an tsara hanyoyin da gwamnatin kasar Jamus zata taimaka wajen shawo kan matsalar.

“Gwamnati ta bayyana bacin ranta, ran yan Najeriya ma ya baci har wasu na kiran gwamnati ta kwace kamfanonin, amma a yanzu gwamnati ta fara fahimtar yadda lamarin yake, saboda idan har zata kwace kamfanoni sai ta biya kamfanonin kudin da suka sayesu tun da farko.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel