Zamu Taimaka Wajen Rage Tsadar Kayyayakin Masarufi a Nigeria

Zamu Taimaka Wajen Rage Tsadar Kayyayakin Masarufi a Nigeria

  • 'Yan Nigeria na fama da hauhauwar farashin kayyakin masarufi, tun bayan bullar cutar corona da tashin dala a kasuwar duniya
  • Abu ne sannan ne kan yadda duk lokacin da kaje kasuwa sai kaji karin kudi kan abunda ka siya a baya
  • Hauhauwar farashi ta shafi ababen more rayuwa da dama, wanda har da ta kai wasu na kasa mallakar abun da suke tasa'arrufi da shi a da

Abuja - A ranar Alhamis din nan ne ministan ayyukan noma a Nigeria ya ce gwamnatin tarayya na mai-yiwu wajen an samu saussauci kan hahauwar farshi a fadin kasar.

Ya ce Yan Nigeria sun dukufa sosai akan noman rani, wanda hakan zai tabbatar da samun abinci da kuma rage tsadar sa.

Ministan ya bayyana hakan yayin da yake kare kasafin kudin ma'aikatar sa a gaban kwamitin da kula da ayyukan aikin gona kamar yarda jaridar The Punch a rawaito.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

Ministan Noma
Zamu Taimaka Wajen Rage Tsadar Kayyayakin Masarufi a Nigeria
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan yace matsalar abinci ko karancinsa, wata babbar matsala ce wacce ta fi matsalar rashin tsaro, yana mai cewa:

In ba abinci, akwai matsala . wannan yanayin na tsadar abinci ba wai iya Nigeria ba ne, muna yin duk abinda zamuyi wajen ganin mun bunksa tare da taimakawa wajen ganin mun saukaka al'ummar kasa

Shugaban kwamitan Alh. Munnir Dan-Agundi yace

Mu duba tare da shiga lamarin, kuma mun hada karfi wajen ganin an tabbatr da wannan kasafin, bayan da muka kai ziyara wasu ma'aikatu da suke kasan wannan ma'aikatar noma

Kwamitin majalissar yayi murna tare da nuna farin cikin sa kan yadda kasafin kudin ya maida hankali kan kananun ma'aikatu da kuma wasu hanyoyi da dabaru wajen magance matsaltsalon kasafin kadu da ake fama da shi a koda yaushe.

Kara karanta wannan

Yan Ta’adda Sun Dasa Bam Ta Karkashin Kasa a Kaduna, Mutum 2 Sun Halaka

Shugaba Buhari Ya kaddamar da Kasafin Kudin shekarar 2023

In za'a iya tunawa dai shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi a gaban majalissar kasa a watan da ya gabata, wanda adadinsa ya kai kimanin tiriliyan 16 da diggonni.

Yan adawa da kuma yan kasa dai na sukar hugaban bisa gabatar da wannan kasafin, wanda suke cewa kudaden da yawa sun tafi ne wajen tafikantar da gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida