An Haramta Kiwon Shanu Da Dare A Wata Shahararriyar Jihar Arewa

An Haramta Kiwon Shanu Da Dare A Wata Shahararriyar Jihar Arewa

  • Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar haramta kiwon shanu a fadin jihar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe
  • Gwamnatin ta kuma hana zirga-zirga da shanu tsakanin kananan hukumomin jihar daga watan Oktoban 2022 zuwa Janairun 2023
  • Gwamnatin ta ce ta dauki wannan matakan ne domin dakile rikici tsakanin makiyaya da manoma a sassan jihar

Gombe - Majalisar Zartawar na Jihar Gombe a ranar Talata ta amince da haramta zirga-zirga da shanu daga wasu jihohi zuwa jihar da kiwon dare.

Taron da Gwamna Muhammadu Yahaya ya jagoranta, kuma ta haramta zirga-zirgan shanu daga karamar hukumar guda zuwa wata daga Oktoban 2023 zuwa Janairun 2023.

Gombe Map
An Haramta Kiwon Shanu Da Dare A Wata Shahararriyar Jihar Gombe. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da ya ke jawabi a wurin taron, Kwamishinan noma da kiwon dabobi, Muhammad Gettado, ya ce an hana kiwon dare daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Kara karanta wannan

Mummunar Gobara Ta Yi Ajalin Bayin Allah Sama da 10 a Kano

Dalilin haramta kiwon dare da zirga-zirga da shanu

A cewarsa, an dauki wannan matakin ne domin rage rikici tsakanin manoma da makiyaya, yana mai cewa akwai bukatar tabbatar da cewa ba a rasa abinci a jihar ba, duba da halin da ake ciki.

Ya ce:

"Majalisar ta amince da matakan dakile rikici tsakanin makiyaya da monama a jihar Gombe. Kamar yadda ka sani, makiyaya suna zuwa daga wasu jihohin suna wucewa ta Gombe.
"A yanzu kashe 35 zuwa 40 na manoman jihar Gombe, da wasu jihohin arewa ba su da abin da za su ci, sun cinye abin da suka noma don kashe 10-15 na abin da ya kamata su samu suka noma. Don haka, akwai bukatar gwamnati ta dauki tsauraran matakai don kula da kankanin abin da manomanmu ke da shi.
"Majalisar zartarwa ta jiha ta amince da haramta wa makiyaya shigowa Gombe daga Oktoban 2022 zuwa Janairun 2023 kuma muna niyyar hana yawo da shanu daga karamar hukuma zuwa wata domin saboda mafi yawancin barnar shanun Gombe ke yi. Abin ya tsaya a kananan hukumominsu har 31 ga watan Janairun 2023."

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Ya cigaba da cewa:

"Kiwon dare na cikin matsalar da muke samu tsakanin manoma da makiyaya, yana da hatsari musamman daga 6 na yamma, a kan lalata amfanin gona, ba kiwon dare daga 6 na yamma zuwa 6 na safe a Gombe."

Kwamishinan ya ce sun umurci shugabannin Miyetti Allah su tabbatar ba a kyalle yara suna kiwon shanu ba don yana daga cikin abubuwan da ke janyo rikicin makiyaya da manoma.

Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifakin haramta kiwon shanu a fili

Kungiyar Gwamnonin Najeriya a ranar Alhamis ta yi ittafaki kan "bukatar samar da sabbin hanyoyin kiwon shanu domin maye gurbin kiwo a fili, da dare da kuma kiwon shanun da kananan yara ke yi a fadin tarayya."

A takardar da kungiyar ta saki bayan zamanta na 25 kuma shugabanta, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya rattafa hannu, gwamnonin sun yi shawaran "samar da hanyoyin aiwatar da shirin da kwamitin sauya salon kiwo a fadin tarayya ta kawo."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel