Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifakin haramta kiwon shanu a fili
- Kamar yadda gwamnan Kano ya fada, zamanin kiwo a fili ya wuce
- Gwamnonin Najeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka wajen samar da sabon hanyar kiwon
Kungiyar Gwamnonin Najeriya a ranar Alhamis ta yi ittafaki kan "bukatar samar da sabbin hanyoyin kiwon shanu domin maye gurbin kiwo a fili, da dare da kuma kiwon shanun da kananan yara ke yi a fadin tarayya."
A takardar da kungiyar ta saki bayan zamanta na 25 kuma shugabanta, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya rattafa hannu, gwamnonin sun yi shawaran "samar da hanyoyin aiwatar da shirin da kwamitin sauya salon kiwo a fadin tarayya ta kawo."
Gwamnonin sun yi ittifakin magance matsalar rashin tsaro wanda ke da nasaba da Makiyaya masu aikata na'ukan laifuka daban-daban, Channel TV ta ruwaito
Amma gwamnonin sun nuna rashin amincewarsu da irin tsangwamar da ake yiwa wata kabila a kasar nan kuma hakan ya sa suka shirya taron na gaggawa.
"Kungiyar na girmama hakkin kowa na zama inda ya ga dama a kasar nan kuma tana Alla-wadai da aikata ta'addanci da kuma tsangwamar wata kabila sakamakon rikicn makiyaya da manoma," wani sashen takardan yace.
KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari da Makinde a kotu kan rikicin makiyaya a Oyo
KU KARANTA: Disamba 2020: Kason da kowani bangare ya kwashe daga N601.11bn na kudaden da FG ke rabawa duk wata
A bangare guda, biyo bayan hauhawar matsalolin tsaro a kasar, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a ranar Juma’a, 12 ga watan Fabrairu, ta zargi wasu dattawan Yarbawa da kokarin tayar da rikici da haifar da fargaba a tsakanin mutane.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa kungiyar wacce ta yi zargin a wata wasika da ta rubuta wa Majalisar Dinkin Duniya ta lura cewa an yi hakan ne don haifar da rikici a tsakanin kungiyoyi da yankuna.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed, kakakin kungiyar NEF, ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar barazana daga mutane, suna kamun kafa da kasashen duniya, don haifar da rikici a cikin kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng