Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matar Kwamandan NSCDC A Nasarawa

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matar Kwamandan NSCDC A Nasarawa

  • Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace matar kwamandan hukumar NSCDC kuma sun harbi kaninsa
  • Kakakin hukumar na jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma yace sun bazama nemansu
  • An garzaya da kanin da aka harba asibiti don ceton rayuwarsa a garin Lafiya dake Nasarawa

Lafia - Yan bindiga sun sace matar Kwamandan sashen leken asiri na shugaban hukumar Sibil Defens, DC Apollos Dandaura, a garin Lafiya, birnin jihar Nasarawa.

An tattaro cewa yan bindigan dauke da bindigogin AK-47 sun dira gidan matar ne suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin sukayi awon gaba da ita.

Vanguard ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ita ne a unguwar Shenge dake garin Lafian Bare-bari.

NSCDC
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matar Kwamandan NSCDC A Nasarawa

Rahoton Daily Trust yace kanin kwamandan wanda shima jami'an hukumar NSCDC ne ya jikkata a harin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun gamu da ajali, jami'an tsaro sun ragargaje su a wata jiha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An garzaya da shi wani asibiti don jinya raunukan da ya samu.

Kakakin hukumar yan NSCDC na jihar, Mr Jerry Victor, wanda ya tabbatar da aukuwan lamarin yace har yanzu shiru basu san inda suka kaita ba.

A cewarsa, hukumar tuni ta tura jami'anta wajen don ceto matar da kuma kama yan bindigan.

An Kama Jami'in Sojan Bogi Da NSCDC a Nasarawa

A wani labari Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC sun yi nasarar kama wani sojan bogi mai shekaru 32 a Jihar Nasarawa.

The Punch ta rahoto cewa an kama wanda ake zargin, Moses Ayaka, a karamar hukumar Lafia, babban birnin jihar.

Kafin kama shi, wanda ake zargin, an ce ya dade yana damfarar mazauna garin.

Ayaka da kansa ya bayyana cewa ya damfari fiye da mutane 22 ya kwace musu kudi da ya kai N440,000.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace dan takarar majalisa na jihar Zamfara

Rundunar ta ce za a mika shi hannun yan sanda domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da shi a gaba kotu ya girbi abin da ya shuka.

Kano: Saboda Budurwa, Asirin Wani Da Sojan Bogi Ya Tonu, An Kama Shi Da Bindiga Da Harsashi

A wani rahoto mai kama da wannan, An kama wani mutum da ake zargi, da ba a riga an bayyana sunansa ba a Kano dauke da bindiga da albursai da kayan sojoji a Kano, Daily Trust ta rahoto.

An gano cewa wanda ake zargin yana basaja ne a matsayin soja, da suna M.A. Ibrahim, kuma yana kwatar kudade hannun mutane kan hanyar BUK road a jihar.

Shaidan gani da ido wanda ya nemi a boye sunansa ya ce wanda ake zargin yana zama ne a unguwar Danbare kusa da BUK, kuma ya rika fada wa mutane cewa shi kyafin ne a rundunar sojojin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel