Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dan Takarar Majalisa Na ADC a Zamfara

Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dan Takarar Majalisa Na ADC a Zamfara

  • 'Yan bindiga sun yi awon gaba da dan takarar mamban majalisar dokokin jihar Zamfara, Suleiman Abdulrahman.
  • An sace Abdulrahman ne a kan hanyarsa ta zuwa jihar Sokoto karbo takardunsa a jami'ar Danfodio
  • A makon nan ne aka kashe wani limami da wasu mutane biyu a jihar Zamfara, lamarin da ya tada hankali

Shinkafi, jihar Zamfara - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da dan takarar majalisar dokokin jihar Zamfara na jam'iyyar ADC a mazabar Shinkafi a zaben 2023, Suleiman Abdulrahman.

An sace shi ne a hanyar Shinkafi zuwa Sokoto a ranar Litinin da yamma a kan hanyarsa ta karbo takardunsa a jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto, TVC News ta ruwaito.

Majiyoyi sun shaidawa gidan talabijin din cewa, 'yan bindigan sun kira ahalinsa, sun kuma shaida musu halin da yake ciki.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya samu nakasu a Sokoto, manyan jiga-jigai sun koma APC

An sace dan takarar majalisar dokoki
Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dan Takarar Majalisa Na ADC a Zamfara | Hoto: tvcnews.tv
Asali: UGC

Sai dai, rahoton da muke samu ya ce basu tambayi kudin fansa ba tukuna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana kai munanan hare-hare yankunan Zamfara

Wannan lamari dai na zuwa ne kasa da sa'o'i 48 bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe wani Limami da wasu mutane biyu a yankin Yankaba a karamar hukumar Kaura Namoda.

Shinkafi dai wata karamar hukuma ce da ke iyaka da karamar hukumar Kaura Namoda, dukkansu suna Arewacin jihar Zamfara ne.

Wadanann yankuna na daga cikin yankunan da 'yan bindiga suka addaba, duk da cewa sun yi yarjejeniyar zaman lafiya da kasurgumin dan bindiga Bello Turji da 'yan tawagarsa a kwanakin baya.

Ya zuwa yanzu dai 'yan sanda basu fitar da wata sanarwa don tabbatar da sace wannan dan siyasa ba.

Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro tare da yawaitar hare-hare daga 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara Ahmad Sani Ya Rasu

A wani labarin, shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Zamfara, Ahmad Sani Kaura ya riga mu gidan gaskiya, Channels Tv ta ruwaito.

An ruwaito cewa, ya yanki jiki ya fadi ne a ranar Laraba a Gusau yayin wani taron zaman lafiya da aka gudanar da majalisar Ulama kan zaben 2023 mai zuwa.

Jigon na PDP a jihar, Aminu Umar ya bayyana cewa, Kaura ya kasance ba shi da lafiya, kuma bai murmure ba lokacin da ya halarci wannan zama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel