Kano: Saboda Budurwa, Asirin Wani Da Sojan Bogi Ya Tonu, An Kama Shi Da Bindiga Da Harsashi

Kano: Saboda Budurwa, Asirin Wani Da Sojan Bogi Ya Tonu, An Kama Shi Da Bindiga Da Harsashi

  • Jami'an tsaro a Jihar Kano sun kama wani mutum da ya dade yana yi wa sojoji sojan gona da sunan M.A. Ibrahim dauke da bindiga, harhsashi da unifom din sojoji
  • Wasu mazauna Kano da suka shaida yadda abin ya faru sun ce mutumin ya tafi ofishin Hisbah ya yi harbe-harbe saboda an kama budurwarsa
  • Bayan hakan ne yan Hisbah suka saki budurwar amma suka dauki hotonsa suka kai wa yan sanda su kuma suka kai kara gidan soja nan aka gano ashe ba soja bane

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - An kama wani mutum da ake zargi, da ba a riga an bayyana sunansa ba a Kano dauke da bindiga da albursai da kayan sojoji a Kano, Daily Trust ta rahoto.

An gano cewa wanda ake zargin yana basaja ne a matsayin soja, da suna M.A. Ibrahim, kuma yana kwatar kudade hannun mutane kan hanyar BUK road a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda Shehin Malami ya Taimaki Wanda Bai Sani ba, Ya Kare da Halaka shi

Sojan Bogi A Kano
Saboda Budurwa, Asirin Wani Da Sojan Bogi Ya Tonu A Kano, An Kama Shi Da Bindiga Da Harsashi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidan gani da ido wanda ya nemi a boye sunansa ya ce wanda ake zargin yana zama ne a unguwar Danbare kusa da BIK, kuma ya rika fada wa mutane cewa shi kyafin ne a rundunar sojojin Najeriya.

An gano cewa an kama wanda ake zargin ne bayan ya tafi ofishin Hisbah ya nemi dole a sako budurwarsa da aka kama. An ce ya yi harbi a iska a ofishin Hisban kuma ya karbo budurwar.

Shaidan gani da ido ya magantu

Shaidan ya ce:

"Ka san Hisbah sun taho nan sun kama mata da ke shan kwaya da wasu ababe marasa kyau. An kama budurwarsa an tafi da ita ofishinsu. Da ya isa ofishin Hisbah a Danbare, ya yi harbi fiye da uku a iska kuma ya tafi da ita.
"Da yan sanda suka kai kara a barikin Janguza. Aka aika da hotonsa sai suka gane ba soja bane, suka bada umurnin a kira su duk inda aka gan shi. Da muka ga motarsa a gidan mai, nan take muka kira su kuma suka kama shi," in ji shaidan ganin idon.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Mutumi Ɗauke Da Bindigu Zai Kai Su Kano

Ya ce duk da cewa ba a kama wanda ake zargin cikin motarsa ba, an gano bindiga da unifom din sojoji a cikin motarsa.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin soji na Kano amma ba a yi nasara ba don wayarsa na kashe a lokacin hada wannan rahoton.

Tsokacin kakakin yan sanda kan lamarin

A bangarensa kakakin yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ya ji labarin kama wanda ake zargin amma ba a riga an damka shi hannunsu ba.

Ya yi alkawarin zai bada karin bayani nan gaba.

Mun yi farin cikin samun labarin kama sojan na bogi, Mazauna Unguwa

Wakilin Legit.ng ya samu ji ta bakin wata mata da ke shagon siyar da kayan masarufi a Danbarre kusa da BUK, amma ta bukaci a boye sunanta saboda dalilan tsaro.

Ta bayyana cewa tabbas ta san shi a unguwar kuma ya saba cin zalin mutane musamman matasa ma duk suna tsoron shin don haka sun yi murnar jin labarin kama shi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan ta'addan ISWAP sun sace manoma a gonakinsu a jihar Borno

A cewarta an gano cewa har motar da ya ke hawa ma ashe ba tashi bane na sata ne.

Kalamanta:

"Ya saba zaluntar mutane da sunan shi soja ne. Matasan wurin sun san shi kuma tsoron shi suke yi sosai.
"Yana ikirarin shi kyaftin ne ashe karya ne. Hatta motar da yake hawa an gano cewa ta sata ce.
"Ya kwace ta ne daga wani. Mun ji dadin wannan kamen, Allah ya kara tonawa irinsu asiri."

An kama sojan gona da kayan hukumar FRSC dauke da katin shaidar aikin soja a Kano

A wani rahoton, jami'an hukumar FRSC da yan sanda sun kama wani mutum mai suna Injiya Gude Ude a jihar Kano da kayan jami'an hukumar kiyaye hadura FRSC kuma dauke da katin shaidar aikin sojan a garin Kano.

Sanarwan da hukumar FRSC ta bayar mai dauke ta sa hannun mukadashin Secta Kwamanda, Ahmed T. Mohammed ta cean kama Ude ne a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2018 a titin Kaduna - Kano a yayin da rundunar ke gudanar da wata kewaye na musamman da akayi wa take da "Operation Zero"

Asali: Legit.ng

Online view pixel