Bidiyo: Matashiya Yar Shekaru 40 Ta Koka Saboda Rashin Mijin Aure, Ta Roki Allah Ya Kawo Mata Agaji

Bidiyo: Matashiya Yar Shekaru 40 Ta Koka Saboda Rashin Mijin Aure, Ta Roki Allah Ya Kawo Mata Agaji

  • Wata matashiya ta je shafin soshiyal midiya don nuna bakin cikinta kan rashin samun mijin aure
  • A cewar budurwar mai shekaru 40, har yanzu bata mallaki da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye a yanzu haka
  • Masu amfani da shafukan soshiyal midiya sun yi martani a kan korafinta inda suka karfafa mata gwiwa

Wata matashiyar budurwa mai shekaru 40 ta koka kan cewa bata jin dadin yadda abubuwa ke tafiya a rayuwarta.

Da take wallafa bidiyo a TikTok cike da rudani, budurwar ta rubuta cewa bata da haihuwa ko miji.

Budurwa
Bidiyo: Matashiya Yar Shekaru 40 Ta Koka Saboda Rashin Mijin Aure, Ta Roki Allah Ya Kawo Mata Agaji Hoto: @user5541238600873
Asali: UGC

Budurwar ta kara da cewa bata da wani tsayayyen namiji a yanzu haka sannan ta roki Allah da ya kawo mata dauki.

"Shekaruna 40 yanzu, ba da, ba miji, babu wani tsayayye da muke soyayya a yanzu haka. Ya Allah ka taimake ni," ta rubuta a bidiyon mai taba zuciya.

Kara karanta wannan

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama'a sun karfafa mata gwiwa yayin da suke martani ga bidiyonta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Lina Lina66158 ta ce:

"Kada ki cire tsammani mama...ina da wata kawa shekarunta 48. Kuma Allah ya nuna buwaya a gareta. Yanzu tayi aure da yara biyu."

Lawon9676yolo ya ce:

"Allah Ubangiji zai share maki hawayenki sannan ya baki burin zuciyarki.
"Komai zai daidaita ."

secure the bag ya ce:

"Alfarmar ubangiji ya isa gareki mama ki yi imani da Allah madaukakin sarki."

jerrybenzo ya ce:

"Ina da wani kawu mai shekaru 47 da ke bukatar mata mai irin shekarunki ban sani ba ko kina so, a Lagas yake da zama."

Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo

A wani labarin, wani dan Najeriya mai suna @kanorsamuel223 a Tiktok ya wallafa wani bidiyo na baturiyar budurwarsa a dandalin.

Kara karanta wannan

Shekaruna 40, Babu Mashinshini Balle In Haihu, Budurwa Ta Koka a Bidiyo

A daya daga cikin hotunan an gano kyakkyawar budurwar tana amfani da tukunyar gas yar tsuguno don soya ayaba. Kuma ga dukkan alamu ta iya aikin gida sosai.

Ba don kalar fatar jikinta ba, mutum zai zata yar Najeriya ne duba ga yadda ta ke gudanar da harkokin girke-girkenta.

Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi na matashin don tambayarsa yadda aka yi ya samu wannan tsaleliyar budurwa a matsayin masoyiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel