Zaben 2023: Atiku Ya Dira Birnin Amurka Don Yakin Neman Zabe

Zaben 2023: Atiku Ya Dira Birnin Amurka Don Yakin Neman Zabe

  • Yan kwanaki bayan dawowa daga kasar Faransa, Alhaji Atiku Abubakar ya sake tafiya Amurka
  • Wannan karon, dan takaran shugaban kasan yace tabbas ya tafi yakin neman zabensa ne
  • Jam'iyyar PDP ta dakatad da harkokin yakin neman zaben shugaban kasa saboda babban maigida

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, ya dira birnin Washington D.C don yakin neman zaben.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya samu rakiyar tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye, Phrank Shuaibu.

Sauran sune gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal; shugaban marasa rinjaye a majalisa Ndudi Elumelu; tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha; da Imasugbon.

Hakazalika akwai mammalakin gidan talabijin na AIT, Cif Raymond Dokpesi, Osita Chidoka, da sauran su.

Atiku
Zaben 2023: Atiku Ya Dira Birnin Amurka Don Yakin Neman Zabe Hoto: @atiku
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jam'iyyar PDP Ta Dakatad Da Yakin Neman Zabe Saboda Dalili Guda

Atiku ya bayyyana hakan a jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita.

Yace:

"Yanzu na dira Washington D.C don tattaunawa da ganawa da mutane don gina tattalin arziki ga Najeriya da kuma bada tsaro."

Jam'iyyar PDP Ta Dakatad Da Yakin Neman Zabe Saboda Maigida Ya Tafi Amurka

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ta sanar da dakatar da yawon yakin neman zabe saboda dan takararta, Atiku Abubakar, ya tafi Amurka.

A jawabin da Diraktan harkokin kwamitin, Umar Bature, ya fitar, ya bayyana cewa an dakatad da ziyarar da akayi niyyar yi zuwa jihohin Ondo, Kebbi, Ekiti da Bayelsa, rahoton Punch.

An dage su zuwa wani lokacin daban.

Buba Galadima: Kwankwaso Zai Kawo Dukkan Jihohin Arewa a 2023

A wani labarin kuwa, tsohon mai yakin neman zaben Atiku a 2019 Buba Galadima, tsohon mamba a kwamitin yardaddu na jam’iyyar APC, yace Rabiu Kwankwaso ne zai lashe zabe a dukkan jihohin arewa a zaben shugabancin kasa na 2023 dake zuwa.

Kara karanta wannan

An tura N4.6bn wani asusu a mulkin Jonathan, EFCC ta fadi dalilin da yasa bata tuhume shi ba

Kwankwaso shi ne ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP mai alamar abarba, The Cable ta rahoto.

A yayin jawabi a ranar Alhamis a tattaunawarsa da Channels TV, Galadima yace Kwankwaso zai lashe zabe a shiyoyi uku na arewa kuma ya samu kuri’u a inda abokan hamayyarsa ke da karfi.

“PDP bata kan takardar kada kuri’a saboda karfi ta a kudu maso gabas ne wanda kuma Peter Obi suke yi. Wurin da PDP ke da karfi kuma shi ne kudu kudu. Kamar yadda Wike baya goyon bayan Atiku, kudu kudu ta kubuce masa.”

... Yace

Asali: Legit.ng

Online view pixel