ASUU Ta Dawo, Ma’aikatan Asibiti Sun Fara Barazanar Tafiya Yajin Aiki Nan da Kwana 7

ASUU Ta Dawo, Ma’aikatan Asibiti Sun Fara Barazanar Tafiya Yajin Aiki Nan da Kwana 7

  • Akwai yiwuwar manyan malaman lafiya da Ma’aikatan cibiyoyin bincike za su daina aiki a watan nan
  • Shugaban kungiyar SSAUTHRIAI na kasa, ya ba gwamnati mako daya ta biya su hakkokinsu
  • Kabir Mustapha yace suna neman ragowar 40% na alawus din shiga hadari da suke bin gwamnati

Abuja - Manyan ma’aikatan asibitocin koyarwa da cibiyoyin bincike da makarantu da ke karkashin kungiyar SSAUTHRIAI suna neman shiga yajin aiki.

The Cable ta kawo rahoto a ranar Alhamis, 13 ga watan Oktoba 2022 cewa ‘Yan SSAUTHRIAI sun ba gwamnatin tarayya wa’adi na kwanaki bakwai.

Kungiyar tace idan har aka shafe tsawon mako guda ba tare da gwamnati ta biya ma’aikata alawus din shiga hadari da suke bi ba, za su tafi yajin-aiki.

Hukumar dillacin labarai tace shugaban kungiyar na rikon kwarya, Mista Kabir Mustapha ya bayyana wannan a jawabin bayan taron da ya fitar jiya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

‘Yan kungiyar sun shafe kwanaki biyu suna taro na musamman a Kalaba a jihar Kuros Riba.

Mun dade muna neman hakkinmu - SSAUTHRIAI

Kabir Mustapha yake cewa sun yi ta rubutawa gwamnatin tarayya takarda da nufin a biya su wadannan alawus, amma har yau ba a iya biya su hakkinsu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ma’aikatan Asibiti
Likitoci a asibiti Hoto: www.weforum.org
Asali: UGC

An ji shugaban na SSAUTHRIAI yana mai cewa babu tabbacin ‘yan kungiyarsa za su cigaba da zuwa aiki idan dai alawus din ba su fito nan da mako daya ba.

Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar tana neman cikon 40% na alawus na musamman da gwamnati tayi alkawarin za ta biya tun lokacin annobar COVID-19.

Malaman lafiya na barin Najeriya

“Muna neman ragowar 40% na cikon watanni biyu na ‘yan kungiyarmu da aka yi kuskuren biyan 10% na alawus din.

Kara karanta wannan

Bayan An Kai Ruwa Rana, Gwamna Wike Ya Yarda Zai Marawa Atiku Baya da Sharadi

Sannan kungiyar ta koka kan yadda ma’aikatan lafiya musamman kwararru suke fita daga Najeriya domin neman kudi.

Domin magance matsalar Kabir ya yi kira ga gwamnati tayi maza ta fara amfani da tsarin albashin CONHESS kamar yadda aka yi yarjejeniya tun a 2017.

ASUU za ta koma aiki

Bayan watanni takwas yara suna zaune a gidajensu, an ji labari kungiyar ASUU ta janye yajin-aikinta. An cin ma wannan matsaya ne a wajen taron NEC.

Kungiyar ta zauna taro na musamman da shugabanninta a sakatariyarta dake Abuja. Hakan na zuwa ne bayan an kammala taron rassa a ranar Larabar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel