Mummunan Hatsarin Mota Ya Faru A Jigawa, An Rasa Rayyuka

Mummunan Hatsarin Mota Ya Faru A Jigawa, An Rasa Rayyuka

  • Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya ta faru a Jihar Jigawa
  • Mai magana da yawun rundunar tsaro ta NSCDC na Jihar Jigawa, Adamu Shehu ya tabbatar da afkuwar hatsarin
  • Shehu ya ce gudu ne fiye da kima da direban ke yi yasa motar ta kwace masa ya kuma yi karo da bishiya a gefen titi

Jigawa - Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyar Kiyawa zuwa Jahun a Jihar Jigawa.

Kakakin hukumar tsaro ta NSCDC na Jigawa, Adamu Shehu, ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Jigawa
Mummunan Hatsarin Mota Ya Faru A Jigawa, An Rasa Rayyuka. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

A cewar Shehu, hatsarin ya ritsa da wata Toyota mai lamba MGM435XA, da ke dauke da fasinjoji zuwa Maiduguri, Jihar Kano.

Kara karanta wannan

'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga

Ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a kan hanyar Kiyawa zuwa Jahun, ya yi sanadin rasa rayyuka biyu; mace da namiji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda hatsarin ya faru

Ya ce:

"A ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoban 2022, misalin karfe 6 na safe, hatsarin ya faru lokacin da mota ta kwace wa direban sakamakon gudu fiye da kima a kusa da kauyen Katika, ya yi karo da bishiya a gefen titi."

Kakakin na NSCDC ya ce nan take an kai wadanda suka yi hatsarin zuwa cibiyar lafiya bai daya da ke karamar hukumar Kiyawa.

Ya bayyana cewa:

"An tabbatar da biyu sun mutu, yayin da saura har da direban motan suka samu raunuka daban-daban kuma an tura su Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, Jihar Bauchi."

Ya bayyana sunan wadanda suka rasun kamar haka; Muhammad Atiku, 27; da Cecilia Peter, 21.

Kara karanta wannan

Yadda Direban Babban Mota Da Wani Suka Sumar Da Jami'in Kula Da Cinkoson Ababen Hawa A Abuja

Shehu ya kara da cewa rundunar ba ta ji dadin afkuwar lamarin ba kuma ta yi kira ga masu ababen hawa su rika bin dokokin titi su dena gudu fiye da kima.

Mummunan hatsarin mota ya laƙume rayukan mutum 15 a Jigawa

A wani rahoton, Rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Jigawa ta ce a kalla mutane 15 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Lawan Shiisu, a ranar Litinin a garin Dutse ya ce hatsarin ya faru ne a hanyar Achlafiya zuwa Karnaya, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel