Yadda Direban Babban Mota Da Wani Suka Sumar Da Jami'in Kula Da Cinkoson Ababen Hawa A Abuja

Yadda Direban Babban Mota Da Wani Suka Sumar Da Jami'in Kula Da Cinkoson Ababen Hawa A Abuja

  • Kotu a Abuja ta bada umurnin a tsare wani direban babban mota da wani a gidan gyaran hali saboda sumar da jami'in kula da cinkoso
  • Mai shigar da kara ya ce jami'in kula da cinkoson ya tare babban motar ne don duba lafiyarta amma direban ya dauke shi zuwa wani wuri ya lakada masa duka ya sace wayarsa
  • Wadanda aka yi karar sun amsa laifinsu kuma alkalin kotu ya ce a dawo a ranar Juma'a kafin ya yanke hukunci

Abuja - Wata kotu mai daraja 1 a Karu Abuja ya bada umurnin a tsare wasu maza biyu, Mansir Seidu da Abdulazeez Shehu, wadanda aka amsa laifin lakadawa jami'in kula da cinkoso a jihar duka har sai da ya suma.

Kara karanta wannan

Rudani: Bayan dogon nazari, kotu ta wanke Magu daga zargin almundahana

Yan sanda sun gurfanar da Seidu, 29 da Shehu, 28, wanda ke zaune a Idu Depot Abuja, da laifin cin mutunci da hana ma'aikacin gwamnatin yin aikinsa, da raunata shi, makirci da sata, Daily Trust ta rahoto.

Jami'in Kula da cinkoso
VIO yana yi wa wani mai mota tambayoyi a AYA a ranar 21 ga watan Agusta. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun, Malam Inuwa Maiwada, ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar Juma'a don yanke hukunci.

Yadda lamarin ya faru

Tunda farko, masu shigar da kara, Olanrewaju Osho, ya shaidawa kotu cewa a ranar 20 ga watan Satumba, an tsayar da Seidu yayin da ya ke tuka babban mota mai lamba KEF 972 SE a gadan Karu don duba lafiyar motarsa.

Osho ya ce Seidu ya tuka mai karar, Hussain Adema, na hukumar kula da cinkoson titi, zuwa hanyar Abacha Barracks a Abuja ya masa duka sai da ya suma.

Mai gabatar da karar ya ce wanda aka yi karar ya kuma caka wa jami'in kula da cinkoson wuka kafin a kai shi asibiti, har yanzu yana karbar magani.

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

Yan sanda sun ce wanda aka yi karar ya yaga wa mai karar unifom na N27,000 ya sace wayarsa ta N68,500.

An kai korafi ne a caji ofis na Kugbo, Abuja.

Ya ce laifin ya saba wa sashi na 79, 397b, 267, 248, 327, da 289 na dokar Penal Code.

Asali: Legit.ng

Online view pixel