Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Tsaron Ministan Abuja Hari

Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Tsaron Ministan Abuja Hari

  • Wasu yan bindiga sun afka wa jami'an tsaro na babban birnin tarayya Abuja hari a ranar Alhamis
  • Lamarin ya faru ne a yayin da jami'an tsaron suka tafi wani aikin kwace baburan yan acaba a kan hanyar zuwa filin tashin jirage na Nnamdi Azikiwe
  • Adamu Shehu, shugaban hukumar na kula da cinkoson ababen hawa, DRTS a tawagar, ya ce za su murkushe baburan bayan samun izinin kotu

FCT, Abuja - Yan bindiga sun kai wa tawagar ministan Abuja hari a ranar Alhamis a yayin da suke wani aikin takaita zirga-zirgan ababen hawa a kan hanyar zuwa filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikiwe.

An kwace babura na haya (acaba) kimanin guda 100 a yayin atisayen kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

'A Soke EFCC,' Matasan Ibadan Suka Fada Wa FG, Sun Yi Babban Zanga-Zanga

Abuja
Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Tsaron Ministan Abuja Hari. Hoto: @daily_trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Laifukansu sun hada da tuki ta hanyar da ba nasu ba, tuki a kan babban titi da sauransu.

A yayin da tawagar suka iso kusa da wurin wanke mota a Lugbe, wasu daga cikin yan acaban sun tattara kansu sun fara harbin yan tawagar da bindiga da kuma wasu muggan makamai.

Kayayyakin da tawagar suka kwato sun hada da bindiga kirar gida, pistol, adduna da wukake.

Babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da aiwatarwa ga ministar babban birnin tarayya, Ikharo Attah ya yi magana lan lamarin ya ce:

"Mun taho korar yan acaba ne a hanyar shiga filin jirgin saman. Ministan Abuja, Malam Muhammad Bello, ya bada umurnin a kore yan acaba domin an hana su bin manyan tituna amma sau da dama muna ganinsu suna satar hanya a babban titi, suna saba doka, hakan yana cutar da mutane don haka muka zo mu kore su a hanyar zuwa filin jirgin saman."

Kara karanta wannan

Yadda Direban Babban Mota Da Wani Suka Sumar Da Jami'in Kula Da Cinkoson Ababen Hawa A Abuja

Ikharo ya yi tir da harin

Da ya ke tir da harin da aka kai wa jami'an tsaron ya ce:

"A wurin mu wannan ba sabon abu bane, mun saba ana kai mana hari. An sha kai mana hari.
"Kafin a kafa tawagar hadin gwiwa, yan acaba sun sha kawo mana hari, abu ne wanda ya saba faruwa a nan."

Za mu nemi kotu ta kwace baburan kafi mu murkushe su - Shehu

Adamu Shehu, shugaban hukumar na kula da cinkoson ababen hawa, DRTS a tawagar, ya yi kira ga masu babura su dena saba dokokin titi.

Babura da aka kwace
Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Tsaron Ministan Abuja Hari. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

Kalamansa:

"Sako na shine su dena satar hanya domin idan muka gan su za mu kwace baburan su.
"Dukkan baburan da muka kwace a yau, za mu nemi kotu ta kwace su kuma za mu murkushe su baki daya."

Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban kasa hari a Legas

Kara karanta wannan

Rudani: Bayan dogon nazari, kotu ta wanke Magu daga zargin almundahana

A wani rahoton, ana kyautata zaton tituna za su kara cunkoso sakamakon yadda mazauna kusa da wuraren jiragen ruwa suke cike da tsoro, bayan wasu wadanda ake zargin bata-gari ne sun kai wa 'yan kwamitin samar da tsaro na fadar shugaban kasa hari a Apapa.

Kamar yadda bayanai su ka kammala, al'amarin ya faru ne a wuraren gate na biyu, na TinCan Island Port, da ke Apapa, cikin kwanakin karshen mako, Vanguard ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel