Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban kasa hari a Legas

Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban kasa hari a Legas

- Sakamakon cunkoson wuraren jiragen ruwan Apapa, jihar Legas, wanda yayi sanadiyyar rikici, mazauna wurin sun fara tararrabi

- Tun bayan wasu bata-gari sun kai wa 'yan kwamitin samar da tsaro na fadar shugaban kasa hari, har hakan yayi ajalin wani direba

- Sai dai, an ajiye gawar direban a cikin motar sintirin 'yan sanda da daddare, amma zuwa washegari aka nemi gawar aka rasa

Ana kyautata zaton tituna za su kara cunkoso sakamakon yadda mazauna kusa da wuraren jiragen ruwa suke cike da tsoro, bayan wasu wadanda ake zargin bata-gari ne sun kai wa 'yan kwamitin samar da tsaro na fadar shugaban kasa hari a Apapa.

Kamar yadda bayanai su ka kammala, al'amarin ya faru ne a wuraren gate na biyu, na TinCan Island Port, dake Apapa, cikin kwanakin karshen mako, Vanguard ta wallafa.

Ganau sun tabbatar da yadda wani mutum ya rasa ransa sakamakon harbe-harbe, wanda ya yi sanadiyyar lalata motar shugaban jami'an tsaron. Direban wata babbar mota, mai suna Adamu ne ya rasa ransa.

Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban hari a Legas
Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban hari a Legas. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sanatan APC ya fusata da ministan ayyuka, ya alakanta kashe-kashe da miyagun tituna

An bayyana yadda aka nemi gawar direban wacce aka ajiye a cikin motar sintirin 'yan sanda aka rasa washegari.

Kuma kowa ya ga yadda aka harbe direban, kuma ya rasa ransa take anan. Mutane da dama wadanda suka ga yadda al'amarin ya faru, sun zargi 'yan sanda da laifin rashin adalci wurin aiwatar da ayyukansu. lnda wasu ke ganin su suka batar da gawar.

Hakika an ruwaito abubuwa iri-iri a kan abinda ya janyo faruwar lamarin. Wasu sun ce masu kai harin sun fara zanga-zanga ne saboda yadda direbobin manyan motoci suke janyo cunkuso a titunan cikin Apapa, jihar Legas, wanda ake zargin har da laifin 'yan sanda wurin janyo hakan.

KU KARANTA: Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako

An yi kokarin jin ta bakin jami'in hulda da jama'ar yankin, SP Olumuyiwa Adejobi, a kan lamarin.

Amma ba a samu nasara ba. Sai dai wata majiya kusa da ofishinsa, ta tabbatar da cewa an sanar da kwamishinan 'yan sandan, CP Hakeem Odumosu al'amarin, kuma kamar an dauki mataki.

A wani labari na daban, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya musanta labarin kai masa hari da 'yan ta'adda suka kara kai wa tawagarsa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

"Ba a kai masa hari ba, balle tawagarsa," kamar yadda Malam Isa Gusau, hadimin Zulum na harkar watsa labarai ya sanar a wata takarda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel