An samu wani magani da ya nuna alamun warkar da cutar Kansa
- Masana kiwon lafiya a kasar Amurka sun bayyana cewar An samu wani magani da ya nuna alamun warkar da cutar Kansa ga duka yara da manyan
- Wannan maganin zai taimaka wajen magance wasu nau’ikan cutar da suka hada da kansar mama
- Binciken ya tabbatar da cewa maganin ya yi aiki ga kashi 76 cikin 100 na masu dauke da nau’in cutar kansa 17
Wani Binciken masana kiwon lafiya a kasar Amurka ya bayyana cewar gwajin maganin cutar kansa mai suna Larotrectinib ya nuna alamomin magance wasu nau’oin cutar a tsakanin masu fama da ita daga manyan mutane zuwa masu kananan shekaru.
Masana masu binciken sun sanar da samar da maganin ne a wani babban taron cutar kansa da aka gudanar a Amurka.
A taron an bayyana cewa maganin zai taimaka wajen magance wasu nau’ikan cutar da suka hada da kansar mama da ke barazana ga rayuwar mata.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, binciken ya tabbatar da cewa maganin ya yi aiki ga kashi 76 cikin 100 na masu dauke da nau’in cutar kansa 17, da suka hada da kananan yara da manya.
Sannan kashi 79 daga cikinsu sun rayu a tsawon shekara guda, a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da maganin da ake fatar zai warkar da cutar Kansa.
An gudanar da gwajin maganin kan mutane 55 masu dauke da cutar kansa da suka kunshi manya 43 yara kanana 12.
KU KARANTA: Uwar Dangote, Mariya Dantata ta ciyar da gajiyayyu 5000, ta gina Masallaci
Sai dai hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna a Amurka ba ta bada izini soma amfani da maganin ba.
David Hyman da ya jagoranci binciken ya ce Maganin zai kasance na farko a duniya da zai kawo sauki a rayuwar manya da kananan yara da ke fama da radadin cutar Kansa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wai shin yaya zaku ji 'yan Najeriya idan Tramp ya kai haren bam ga 'yan ta'adda Boko Haram kamar yadda ya yi a kasar Syria?
Asali: Legit.ng