Fashewar Tanka Ta Halaka Rayukan Mutane, Wasu Sun Jikkata a Ogun

Fashewar Tanka Ta Halaka Rayukan Mutane, Wasu Sun Jikkata a Ogun

  • Wata tanka makare da man fetur ta fashe yayin sauka daga hawa a yankin Ilo Awela dake babban Titin Legas zuwa Abeokuta a jihar Ogun
  • Hukumar kiyaye hadurra reshen jihar tace zuwa yanzun an ceto mutum uku yayin da wasu biyu suka kone kurmus, kana motoci 12 lamarin ya taba
  • Tuni dai jami'an kwana kwana suka kewaye wurin da lamarin ya faru domin kiyaye sake samun hadari bisa rashin sani

Ogun - Mutum biyu sun ƙone ƙurmus, wasu uku sun jikkata yayin da Motoci 12 suka lalace a wata fashewar Tanka da Safiyar Alhamis ɗin nan a yankin Ilo Awela dake kan babban titin Lagos -Abeokuta.

Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar kiyayen haɗurra (FRSC) reshen jihar Ogun, Misis Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Abeokuta, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Jagoran Al'umma a Jihar Arewa

Haɗarin Tanka a Ogun.
Fashewar Tanka Ta Halaka Rayukan Mutane, Wasu Sun Jikkata a Ogun Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

A jawabinta, Okpe tace

"FRSC ta kai agaji da misalin karfe 1:30 na wayewar garin Alhamis a wani haɗari da ya rutsa da Tanka maƙare da Man Fetur, yayin da take gangarawa daga hawa a mahaɗar Titin Abeokuta– Lagos, ta faɗi kuma ta fashe."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Nan da nan aka nemi jami'an kwana-kwana kuma aka mamaye wurin domin daƙile samun wata matsalar a gaba. Zuwa karfe 4:05 na Asuba adadin motoci 12 lamarin ya shafa."
"An Ceto mutum uku yanzu haka suna kwance a babban Asibitin Ota, matasa maza biyu matashiyar mace. Gawarwakin mutum biyu sun ƙone ta yadda ba za'a gane su ba, an ɗauke su daga wurin."

Menene ake zargin ya haddaa wannan hadari?

Mai magana da yawun hukumar FRSC din ta kara da cewa ana zargin gazawar innin Tankar ne ya haddasa hadarin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rudani: Bayan dogon nazari, kotu ta wanke Magu daga zargin almundahana

A wani labarin kuma Wani Fitaccen Malamin Musulunci Da Dalibansa Sun Nutse a Ambaliya a Kwara, Allah ya musu rasuwa

Wani shahararren Malamin Islama a jihar Kwara, Sheikh Abdulganiyu Nuraini, ya rasu sakamakon Ambaliyar ruwa.

Bayanai sun nuna cewa ruwan ya yi awon gaba da motar Malamin tare da wasu ɗalibansa biyu lokacin da zaau tsallaka wata gada a Ilorin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel