Abubuwa 9 da Mata Basa So Daga Namiji da Ya Kamata Kowa Ya Sani

Abubuwa 9 da Mata Basa So Daga Namiji da Ya Kamata Kowa Ya Sani

  • Mata sun bayyana kadan daa dabi'un maza da suke ganin bai dace ba, lamarin da ya jawo cece-kuce a shafin intanet
  • Da yawan mata sun bayyana cewa, sun tsani maza masu kazanta, musamman wadanda ke tara faratu doraye da kuma masu tsamin hammata
  • Wasu matan kuma sun ce, ba sa son namiji mai yawan surutu, masu huda jikinsu, masu dafewar hakora da kuma wadanda ba 'yan kwalisa ba

Mai amfani da shafin sada zumunta, Thapz ya tambayi mata a Twitter su bayyana abubuwan da ba sa so a jikin namiji, lamarin da ya jawo martani da maganganu masu zafi a Twitter.

Kama daga dabi'u, fita ta jiki har zuwa halaye, mata sun tofa abinda ke zukatansu, inda suka bayyana ababen da basu so game da maza.

Halaye da dabi'u 9 da mata basu so a tattare da namiji
Abubuwa 9 da Mata Basa So Daga Namiji da Ya Kamata Kowa Ya Sani | Hoto: Galaxy Television
Asali: UGC

Ga abubuwa tara da mata suka ce basu so daga namiji

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tashi mazauna kauye, suka hallaka mutum 19 a Arewa

@DuchessWakanda tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Rashin tsafta (ciki har da dogin faratun hannu), rashin mtuntawa, yawan alkawari babu cikawa."

@Ayanda_Yandiey tace:

"Wari mai tsanani"

@Masondoma tace:

"Mutumin da ke alfahari da kudinsa, motocinsa da gidajensa. Bana son irin wanna ko kada."

@WeedroseP1 tace:

"Namijin da zai wuni yana magana kamar ma'aikacin gidan rediyo."

@NgwanaMopedi tace:

"Wanda bai da kudi."

@Thandolwethu tace:

"Haka kawai yazo ya yi maka alkawarin da baka tambaye shi ba mma ya ki cikawa."

@GeeYew6 tace:

"Mai kwanji a ciki."

@IamNdumy tace:

"Mara mutunci, mara natsuwa kuma mai surutu.

@Neheng tace:

"Mai busassun labba."

@Binnie_Shuga tace:

"Mai warin baki."

@Lindi_Amaira tace:

"Mai dogayen faratu, mai sanya dan kunne, Mohawk, mai dasashen hakora, kazami, mara ko kobo, mai sanya wandon da ke rufe safa.

@Luu6Luthando tace:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ISWAP ta kai kazamin hari kan sansanonin soji a Borno, an hallaka sojoji da yawa

"Mutumin da zai daura hotonki a soshiyal midiya."

Bidiyon Budurwa Na Tafiya da Zakuna Kamar Karnuka Ta Jawo Cece-Kuce a Intanet

A wani labarin, wata budurwa a TikTok mai suna @ituhadebetsubane ta yada wani bidiyonta a kafar sada zumunta na yadda ta kasance tare da wasu zakuna a gidan ajiye dabbobi.

A bidiyon da miliyoyin jama'a suka gani a kafar, an ga budurwar na rike da sanda yayin da ta saka wasu manyan zakuna uku a gaba.

Kasancewar tana rike da sanda, an ga tana tafiya a bayansu, su kuwa suna gaba kamar dai mai kare da karnukansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel