Malamin Musulunci Ya Yi Bayanin Hukuncin Yajin aiki, Ya Wanke ASUU Daga Zargi

Malamin Musulunci Ya Yi Bayanin Hukuncin Yajin aiki, Ya Wanke ASUU Daga Zargi

  • Malaman jami’a sun dauki sama da watanni bakwai suna ta yajin-aiki a karkashin kungiyarsu ta ASUU
  • Ganin haka ya sa wani mutumi ya tambayi malaman adini game da hukuncin cin albashi alhali ana yajin-aiki
  • Dr. Abdallah Gadon Kaya wanda shi ma malamin jami’a ne, yace ASUU ba ta saba doka, da ta daina shiga aji ba

Kano - A ranar Asabar da ta wuce, 24 ga watan Satumba 2022, aka jefawa Abdallah Usman Gadon Kaya tambaya game da yajin-aikin malaman jami’a.

Wani mutum ya tambayi Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya bayan ya kammala karatu, game da hukuncin a biya malaman jami’a albashi alhali suna yajin-aiki.

Shehin malamin ya fara da matashiyar cewa babu mamaki an aiko masa da wannan tambaya ne domin an san shi ma yana koyarwa a jami’ar tarayya a Kano.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi Ya Ragargaji Gwamnatin APC a gaban Majalisar Dinkin Duniya

A bidiyon da aka fitar, Sheikh Abdallah Gadon Kaya yace a iyaka saninsa, babu wata dokar kasa ko ta addini da za ta hana ma’aikaci ya fito neman hakkinsa.

Neman hakki ba sabon Allah ba ne

Malamin yake cewa a iyakar ilminsa, yajin-aiki yunkuri ne da ma’aikata ke yi wajen taso gwamnati a gaba, a fatawarsa, yace babu abin da zai haramta yajin-aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abdallah Gadon Kaya ya dauko dogon bayani a game da abin da ya jawo malaman jami’a da ke karkashin kungiyar ASUU suke yajin-aiki tun farkon shekara.

Abdallah Gadon Kaya
Sheikh Abdallah Gadon Kaya Hoto: Martaba FM
Asali: UGC

“A sani cewa, su ma’aikatan jami’a, suna tafiya ne a bisa tsarin gwamnatocin kasar da suke rayuwa.
“Duk ma’aikatu na gwamnati a Najeriya suna da dokoki da kuma tsare-tsare da ke gudana a cikinsu.”

- Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata

A matsayinsa na malamin addini, Gadon Kaya yace bai da masaniya sosai a kan sha’anin, amma ya kafa hujja da bayanan da ake yi masu a wajen taron ASUU.

A fatawar malamin, yace babu wani wanda ya isa yace bai halatta a nemawa dalibai ‘yanci ko a inganta jami’o’in gwamnati ba, wanda hakan ne manufar ASUU.

Haka zalika Sheikh Gadon Kaya yace ba za a haramtawa ma’aikaci ya nemi bukatarsa a wajen gwamnati ba, muddin hakan bai ci karo da dokar kasar ba.

Dr. Gadon Kaya yace abin da ya sa suke yajin-aiki sun hada da karancin dakunan dalibai da wurin karatu da rashin albashi da sauran abubuwan jin dadin aiki.

Sai dai malamin yace wani zai iya yi masa raddi, amma shi abin da ya fahimta da mas’alar kenan. A karshe ya yi kira da a biya su duk albashin da aka hana su.

Matsayin Dattawan Arewa

An ji labari Hakeem Baba Ahmed yace ba za su zama ‘Yan kallo a 2023 ba, Dattawan Arewa za su fadawa mutane wanda ya fi cancanta su zaba.

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

Dr. Hakeem Baba Ahmed yace za su yi zama da duka masu neman mulki domin gano ‘dan takaran da zai fi taimakon mutanen Arewacin Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel