Yadda Dattawan Arewa Za Su Bi, Su Tsaida 'Dan takararsu na Shugaban kasa Inji NEF

Yadda Dattawan Arewa Za Su Bi, Su Tsaida 'Dan takararsu na Shugaban kasa Inji NEF

  • Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ba za ta sa ido a zaben 2023 ba, za ta shiga domin a dama da ita
  • Dr. Hakeem Baba Ahmed mai magana da yawun NEF yace za su fadawa al’umma wanda za su zaba
  • Kafin a dauki wannan matsaya, kungiyar za ta zauna da duka ‘yan takara, ta ji shirin da suke da shi

Kano - Dr. Hakeem Baba Ahmed shi ne mai magana da yawun kungiyar NEF ta Dattawan Arewacin Najeriya, ya yi magana a game da shirinsu na 2023.

Dr. Hakeem Baba Ahmed ya tattauna batun siyasa da cigaban Arewacin Najeriya a wani zaure a Twitter wanda wani ‘dan jarida, Ameenu Kutama ya tara jama’a.

Kakakin na NEF ya tabbatar da cewa zuwa yanzu ba su da wani ‘dan takara, amma yace kafin zabe za su fadawa al’umma wanda ya cancanta za ba kuri’arsu.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi Ya Ragargaji Gwamnatin APC a gaban Majalisar Dinkin Duniya

Hakeem Baba Ahmed yace ba za su zama ‘yan kallo a zaben shugaban kasa ba, za su zauna da duk masu neman shugabanci domin ganin wanda ya dace da Arewa.

Daga cikin abubuwan da kungiyar NEF za ta duba a ‘yan takaran akwai lafiyar jiki da kaifin kwakwalwa da kuma sanin mafita wajen shawo kan matsalolin kasar.

Mun saurari wannan tattaunawa, inda Legit.ng ta ji Hakeem Baba Ahmed yana mai cewa za su zabi ‘dan takaran da zai kawo gyara, ya taimaki Arewacin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan takarar Shugaban kasa a 2023
Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Kwankwaso Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

Daga yanzu zuwa lokacin zabe, kungiyar dattawan tace tana da watanni biyar domin zama da ‘yan takaran domin jin manfufofinsu, kuma har ta fara wannan shiri.

A abubuwan da NEF za ta tambayi mai neman mulki akwai mutanen da yake da shi wanda za iyi aiki da su a gwamnatinsa idan ya yi nasarar zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2023: Ba Zan Bar 'Ya'Yana Su Fita Zuwa Ƙasashen Waje Ba, Atiku Ya Ɗau Sabbin Alƙawurra

Dattawan Arewan suna ganin wannan tsari da suka dauko zai taimakawa ‘yan takara da masu zabe. A haka ne jama’a za su san manufofin wanda za su ba kuri’arsu.

A jawabinsa, dattijon yace kungiyarsu ta sha bam-bam da Afenifere ko Ohanaeze, yace NEF ba za ta goyi bayan ‘dan takara saboda kurum ‘Dan Arewa ne shi ba.

Sannan mun ji dattawan yace ba za su goyi bayan wanda ba zai taimaki mutanen Arewa ba.

An yi kuskure a baya

A baya dai kun ji rahoto da ya nuna Kungiyar Northern Elders Forum tace sai ta zauna da ‘yan takara kafin ta yanke shawarar wanda za tace a zaba a 2023.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed yace NEF za ta jijjiga 'yan takaran domin ganin ba su maimaita kuskuren da aka yi a 2015 na bin Muhammadu Buhari ido rufe ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel