Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata

Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata

  • Wata matashiya yar Najeriya mai shekaru 23 ta yi kuka har taji babu dadi sakamakon mutuwar mijinta
  • A wani bidiyo da ya wallafa, an gano wasu taron mata tsaye a kanta yayin da ake aske gashin kanta da almakashi
  • Da take juyayin rashin mijin nata, ta tambayi ko yaushe zata samu sauki, tana mai cewa radadin yayi mata yawa

Wata matashiya yar Najeriya mai shekaru 23, ta yi alhinin rashin mijinta a shafin soshiyal midiya bayan ya yi mutuwar faran daya.

An gano matashiyar wacce ke juyayi a cikin wani bidiyon TikTok a yanayi na alhini da hawaye a idanunta yayin da wasu taron mata ke aske mata gashin kanta.

Matashiya
Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata Hoto: TikTok/@chinyeakaarinze
Asali: UGC

Ta koka cewa abun akwai ciwo sosai yadda ya zama bazawara a karancin shekaru irin nata. Ta tambayi dalilin da yasa mutumin bai tsaya ba bayan sun shirya yadda rayuwarsu Za ta kasance.

Kara karanta wannan

Wanka Kullum Asarar Ruwa Ne: Bidiyon Kyakyawar Budurwar da Tayi wata 1 Babu Wanka

“Ya Allah yaushe zan ji daidai? Radadin yayi mun yawa. Zama bazawara a shekaru 23 Arinze ba haka muka tsara da kai ba yaranmu na tambayana kai a kullun, mutuwa me yasa,” ta rubuta a jikin bidiyon.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakonnin ta’aziyya na ta shigowa matar mamacin.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

angelgiftifeanyic ta ce:

"Muna a cikin yanayin amma Allah shine masanin komai, radadin na har abada ne amma ki dunga duba ya Allah kuma ki tuna da yara ki.”

love ta ce:

“Kai. Ina mai baki hakuri yar’uwa kuma ki tuna dole ki zamo mai juriya a yanzu sannan ki kula da yaranki. Suna bukatarki sosai a yanzu.”

Dalency Rita ta ce:

“Ina mai baki hakuri yar’uwa...amma daga bisani ki duba yiwuwar sake aure ba son ranki bane zama bazawara a shekara 23..kina da sauran aiki ja a gabanki.”

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

Wasu Na Kishi: Matashi Ya Jinjinawa Matarsa Yayin da Take Girki Da Icce A Bidiyo

A wani labarin, wasu ma’aurata da suka daura bidiyoyi a TikTok sun haifar da zafafan martani yayin da mijin ya jinjinawa matar tasa a madafi yayin da take girka masu abinci. Yayin da take girki a kan icce, mijin na ta ihun ‘matata’.

Bayan ya yi wannan firucin, ya jaddada kalamunsa na farko yayin da yake kara kuwa.

Yayin da mijin ke jinjina mata, matar ta kalli kamaran cike da mamaki sannan ta dandana abun da take gikawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel