Fitaccen Dan Wasan Najeriya, Ahmed Musa, Ya Kwanta Asibiti, An Masa Tiyata

Fitaccen Dan Wasan Najeriya, Ahmed Musa, Ya Kwanta Asibiti, An Masa Tiyata

  • Likitoci sun yiwa Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Ahmed Musa, tiyata
  • Shahararren dan wasan kwallon kafan ya samu matsala ne a hannunsa na hagu wanda ya kai ga kwantar da shi
  • Jama’a a soshiyal midiya sun yiwa jarumin kwallon kafan fatan alkhairi da addu’an samun lafiya

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa, ya kwanta a asibiti inda likitoci suka yi masa tiyata.

Jarumin kwallon kafan ya je shafinsa na Instagram a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba domin godiya ga Allah kan nasarar da aka samu wajen yi masa aikin a hannunsa na hagu.

Musa ya mika godiyarsa ga hazikan likitocin da aka sanya su yi masa aikin kan namijin kokarin da suka yi wajen inganta masa lafiyar jikinsa.

Ahmed Musa da likita
Fitaccen Dan Wasan Najeriya, Ahmed Musa, Ya Kwanta Asibiti, An Masa Tiyata Hoto: ahmedmusa718
Asali: Instagram

Ya kuma godema dumbin masoya kan sakonni da addu’o’i da kuma kalaman karfafa gwiwa da suka aike masa da shi.

Kara karanta wannan

N797bn: Majalisar wakilai ta shiga damuwa, an kashe kudi, an gaza karasa titin Abuja zuwa Kano

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga karshe, jarumin yace yana fatan komawa filin wasa nan bada jimawa ba cike da karfi da koshin lafiya.

Ya rubuta a shafin nasa:

“Ina son nuna godiyata ga Allah kan nasarar da aka samu wajen yi mani aiki a hannuna na hagu. Kamar yadda duk mukasani, babu siyasa da yake karami don haka ina godiya ga kwararrun likitocin da aka hadani da su kan namijin kokarin da suka yi. Haka kuma gareku duka kan sakonni, addu’o’I da kalaman karfafa gwiwa. Ina fatan dawowa filin wasa kwannan nan cikin karfi da koshin lafiya. Godiya ga kowa. ❤️ "

Jama'a sun yi masa fatan alkhairi

realalinuhu ya yi martani:

"Allah ya baka lafiya namijin duniya "

ayshatulhumairah ta ce:

"Allah Yasa Kaffara ne"

official_mohamedhussein15

"Allah ya tashi kafada dan uwa"

oshaniwa

"Ka dawo da karfi kyaftin"

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mikel Obi, Tsohon Kyaftin Din Super Eagles, Ya Yi Murabus Daga Kwallon Kafa

Jarumin Kwallon Kafa Ahmed Musa Da Mai Dakinsa Sun Samu Karuwar Da Namiji

A wani labarin, mun ji cewa Allah ya azurta Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa tare da matarsa da samun karuwar 'da namiji.

Dan wasan kwallon kafar ya je shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, domin sanar da wannan abun alkhairi da ya samu iyalinsa.

Yayin da yake hamdala ga Ubangiji a kan wannan babban kyauta da ya yi masa, dan wasan ya bayyana sunan jinjirin a matsayin Adam Ahmed Musa amma za a dunga kiransa da Zayd.

Asali: Legit.ng

Online view pixel