Nakiya Ta Tashi a Wani Masallacin Kabul, Mutane 7 Sun Mutu, 41 Sun Jikkata

Nakiya Ta Tashi a Wani Masallacin Kabul, Mutane 7 Sun Mutu, 41 Sun Jikkata

  • Rahoton da muke samu daga kasar Afghanistan ya bayyana cewa, wasu tsageru sun adasa bam a bakin masallaci
  • An samu raunuka yayin wasu mutane sama da 40 suka samu raunuka, an kwantar dasu a asibiti
  • Hukumomin kasar sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma sun ce suna ci gaba da bincike don gano tushensa

Kabul, Afghanistan - Tashin wani bam a wani masallaci a birnin Kabul na Afghanistan ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane bakwai.

AlJazeera ta ruwaito cewa, an tada bam din ne a gefen masallacin Wazir Akbar Khan bayan idar da sallar Juma'a a yau 23 ga watan Satumba.

Yadda aka kai masallaci a Kabul ta Afghanistan
Bam ya tashi a wani masallaci a Kabul | Hoto:aljazeera.com
Asali: UGC

Hakazalika, rahoton ya kuma bayyana cewa, an samu sama da mutane 40 da suka samu munanan raunuka ta sanadiyyar harin.

Martanin hukumomi

Khalid Zadran, mai magana da yawun 'yan sanda a Kabul ya shaida cewa:

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan idar da sallah, a lokacin da mutane ke son fita daga masallaci, bam din ya tashi. Duk wadanda lamarin ya rutsa dasu fararen hula ne."

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta fito ta bayyana alhaki ga kai wannan mummunan hari.

Wani asibitin agajin gaggawa na Italiya ya ce ya karbi mutane 14 hatsarin ya rutsa dasu, kuma nan take hudu daga ciki suka mutu.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Kabul a shafinta na Twitter ta bayyana cewa, wannan mummunan lamari ne mai daga hankali a ci gaba da ta'azzarar rashin tsaro a kasar Afghanistan.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Abdul Nafi Takor ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin.

Sojin Sama Sun Sake Ruwan Bama-Bamai Kan Maboyar ’Yan Bindiga a Zamfara

Kara karanta wannan

Tashin hankali a wata jihar Arewa yayin da 'yan sanda suka kashe matashi dan shekara 16

A wani labarin, rahoton da muke samu ya bayyana cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta sake gano mafakar 'yan ta'adda karkashin jagorancin Dan Karami a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ce, sojojin sun yi nasarar jefa bama-bamai kan mafakar 'yan bindigan da ke addabar jama'ar yankin.

A cewar wata majiyoyi daga yankin, an kashe wasu 'yan bindiga da dama a harin da aka kai jiya Alhamis 22 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel