'Yan Matan Katsina Sun fi Yara Maza Kwazo a Jarabawar WASSCE ta 2021

'Yan Matan Katsina Sun fi Yara Maza Kwazo a Jarabawar WASSCE ta 2021

  • Kwamishinan ilimi na jihar Katsina, Badamasi Lawal, ya sanar da irin hazakar da dalibai mata suka nuna a kan maza a a WASSCE ta 2021
  • Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ce ta biyawa dalibai sama da 18,000 maza da mata kudin jarabawa amma matan 7,000 ne suka rubuta
  • Ya sanar da yadda mafi yawan dalibai matan suka samu cin darasin turanci da lissafi har suka zarce mazan

Katsina - Badamasi Lawal, kwamishinan ilimi na jihar Katsina, ya ce dalibai mata sun nuna kwazo fiye maza a jarabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma (WASSCE) a shekarar 2021, jaridar gazettengr ta rahoto.

Taswirar Katsina
'Yan Matan Katsina Sun fi Yara Maza Kwazo a Jarabawar WASSCE ta 2021. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Lawal ya bayyana haka ne a wajen bikin rufe makarantar koyar da yara mata (GEP-III) a ranar Alhamis a Katsina. Ya kara da cewa hakan ya samu ne sakamakon jajircewar da gwamnati ta yi na karfafa wa ‘yan mata guiwa a jihar ta hanyar shirye-shiryen ilimi daban-daban.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

A cewarsa, a shekarar 2021 dalibai 18,321 suka dauki jarabawar WASSCE, kuma gwamnatin Katsina ta biya kudin jarabawar ga dukkan wadanda suka rubuta.

“A cikin su 10,441 maza ne, yayin da dalibai mata 7,880. Amma abin mamaki, sakamakon ya nuna cewa 4,627 daga cikin dalibai mata ne suka samu nasara a harshen Turanci, wanda ya kai kashi 58.7 cikin 100.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Daga cikin dalibai maza 10,441, 5,632 ne kadai suka samu cin harshen turanci, wanda shine kashi 54 cikin 100. Hakan na nufin ‘yan matan sun fi mazan maki a harshen Turanci.”

- Lawal yace.

A fannin ilmin lissafi, kwamishinan ya bayyana cewa ‘yan matan sun zarce yara mazan saboda 5,678 daga cikinsu sun sami maki, yayin da 4,726 daga cikin mazan ne kawai suka samu makin da ya dace.

Bauchi: Hotunan Makarantar Sakandare Mai Dalibai 1500 amma Babu Bencinan Zama da Bandaki

Kara karanta wannan

"Idan Katsina Za Ta Iya, Ondo Ma Za Ta Yi' - Akeredolu Zai Siya Wa Amotekun Bindiga Duk Da FG Bata Yarda Ba

A wani labari na daban, Hotunan wata makarantar sakandare a jihar Bauchi mai suna Kwalejin koyar da ilimin addinin Islama ta Yakubun Bauchi mai dalibai sama da 1500 amma babu bencina ko bandaki ya ba jama'a mamaki.

Wannan an tattaro shi sakamakon wallafar da TrackaNG, wata kungiyar taimakon kai da kai dake haskowa tare da bankado yadda aka aiwatar da manyan ayyukan gwamnati.

Kamar yadda TrackaNG ta saba, tana nemowa tare da nunawa 'yan kasa yadda ayyukan ko gudana ko akasin hakan kuma sun yi wannan fallasar ne a ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel