Ba Buhari Bane Matsalar Najeriya, Ku Dena Dora Masa Laifi, In Ji Babban Malamin Addini

Ba Buhari Bane Matsalar Najeriya, Ku Dena Dora Masa Laifi, In Ji Babban Malamin Addini

  • Apostle Alfred Williams, babban fasto a cocin Faith Tabernacle ya ce a dena dora wa Shugaba Buhari laifi kan matsalolin kasar
  • Malamin addinin mazaunin Birtaniya ya ce tsarin kasar ne ta hana Buhari samun damar aiwatar da ayyukan alheri da ya yi niyyar yi
  • Williams ya ce muddin ba a sauya tsarin yadda kasar ta ke ba, ko shi, ko sauran manyan malaman addini ne suka zama shugabannin kasa ba za su iya tubuka komai ba

Jihar Ogun - Malamin addini dan Najeriya mazaunin Birtaniya kuma babban fasto a cocin Faith Tabernacle, Apostle Alfred Williams, ya ce kada a dora wa Buhari laifi bisa matsalolin Najeriya

Williams ya ce tsarin yadda Najeriya ta ke ne ke kawo cikas ga kyawawan niyya da Buhari ke da shi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP: An kashe 'yan jiha ta 5000 cikin shekaru 11 a hare-haren 'yan bindiga

Fast Williams
Ba Buhari Bane Matsalar Najeriya, Ku Dena Dora Masa Laifi, Malamin Addini. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi magana yayin ziyara da ya kai gidan talabijin na kasa, NTA, a Abeokuta, Jihar Ogun.

Malamin addinin ya ce tsarin Najeriya ba zai bari kowa ya iya tabbuka komai ba a kasar.

Ya ce:

"Ba Buhari bane matsalar Najeriya. Matsalar tsarin yadda kasar ta ke ne. Idan kai ko ni, fasto ko fasto Adeboye na Redeemed (RCCG), wanda duk muke girmamawa, ko Fasto Kumuyi ya zama shugaban kasa, za su shiga damuwa.
"Don haka, ba mutumin da ke kujerar bane, tsarin kasar ce ke hana mutum aiwatar da niyyarsa ta alheri. Idan muka mayar da hankali kan Buhari, idan wani ya hau kujerar kuma tsarin bai canja ba, zai gaza kamar yadda Buhari ya gaza."

Williams ya ce Najeriya na bukatar shugaban da zai yi wa al'umma hidima a yayin da kasar ke shirin babban zaben shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Majalisa ta tsit, ta gaza sake tado da batun tsige shugaba Buhari

Buhari Ya Nada Kwarrren Dan Jarida Matsayin Sabon Shugaban NTA Na Kasa

A wani rahoton, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada Mr Salihu Abdulhamin Dembos a matsayin direkta-janar/babban shugaba na Gida Talabijin Na Najeriya, NTA.

Ministan Sadarwa da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, The Punch ta rahoto.

Ya ce nadin da aka masa na tsawon shekaru uku ne a karon farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel