Zan Iya Dukan Kirji In Rantse Cewa Mijina Bai Taba Cin Amanata ba, Jarumar Fim

Zan Iya Dukan Kirji In Rantse Cewa Mijina Bai Taba Cin Amanata ba, Jarumar Fim

  • Jarumar fim din kudancin Najeriya, Lizzy Anjorin, ta sanar da cewa zata iya dukan kirji cewa mijinta bai taba cin amanarta ba
  • Jarumar tace mijinta bai cika goma ba kasantuwarsa 'dan Adam, ta san yana da wasu hali amma banda na cin amana da wasu matan
  • Kwanakin baya jarumar ta musanta rade-radin da ake yadawa na cewa mijinta yana da wasu matan, tace bashi da wannan karfin

Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya, Lizzy Anjorin, ta ce Lateef Lawal, mijin ta, bai taba cin amanarta ba tun da suka yi aure.

Anjorin da Lawal sun yi aure a watan Yulin 2020 a wani biki na sirri wanda ya karbi bakuncin 'yan uwa da abokan arziki.

Ma'auratan sun yi haifa ɗansu na farko a watan Mayun wannan shekarar. Sun kuma sadaukar da jaririn bayan wannan watan a Amurka.

Kara karanta wannan

Alkawarin Aure: An Fara Gabatar da Shaidu Kan Hadiza Gabon a Kotun Shari'ar Musulunci

Ma'auratan sun sha fama da cece-kuce da dama tun daga lokacin, TheCable LifeStyle ta rahoto hakan.

Jaruma Lizzy
Zan Iya Dukan Kirji In Rantse Cewa Mijina Bai Taba Cin Amanata ba, Jarumar Fim. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin wani faifan bidiyo da aka yi ta yadawa a soshiyal midiya, Anjorin ta sake yin watsi da rade-radin da ake yadawa kan cin amarar da take fama da shi a aurenta.

Jarumar fim din ta ce "zata iya rantsuwa da komai" kan cewa mijinta Lawal bai taba cin amanarta ba.

Anjorin ta ce kamar kowa, maigidanta na iya kawo matsala amma ba zai taba yi mata yi mata wani abu ba ta hanyar kwana da wasu mata ba.

“Lateef mutum ne mai mutunci har cikin zuciyarsa. Wataƙila yana da wani halin mara kyau, ba wanda yake cikakken mutum. Lawal mai karfin zuciya ne kuma mai taurin kai."
“Amma cewa zai yi min mugun abu ta hanyar kwantawa da wasu mata ba zai yiwu ba. Zan iya rantsuwa da komai tun da muka yi aure, bai taba cin amanata ba, bai kwantaa da wata mace ba.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta haramtawa 'yan Najeriya cin gandan fatar dabbobi, ta fadi dalilai

- Jarumar ta tabbatar.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jarumar ta fito tana kare mijinta a fili ba.

A cikin 2020, Anjorin ta yi watsi da ikirarin cewa Lawal ya auri mace fiye da daya.

“Mijina ba shi da karfin rike mata biyu kada a kai ga maganar shida. Da yake na zama ta jama'a, ya kamata in yi rayuwa ta misali don in kasance mai hankali, da lura da abin da nake yi."

- Lizzy tace.

Da Digirina na Tafi Libya Aikin Goge-goge: Budurwa 'Yar Najeriya da ake Biya N100,000 Albashi

A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya dake gangariyar turanci a yanar gizo ta koka kan yadda masu digiri ke barin Najeriya kuma suke kananan ayyuka a Libya.

A bidiyon budurwar, tace tana da digiri kuma tana bukatar kudi don yin rayuwa mai kyau. Ta sanar da yacca ake biyanta N25,000 a wata lokacin da take koyarwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Budurwar wacce ta lankwasa harshe zuwa ingantaccen turanci domin tabbatar da cewa digiri gareta, ta sanar da cewa tana koyar da ajujuwa shida reras.

Asali: Legit.ng

Online view pixel