Buhari Ya Ba Amurkawa, ’Yan Birtaniya da Sauran Kasashe Takardar Zama ’Yan Najeriya

Buhari Ya Ba Amurkawa, ’Yan Birtaniya da Sauran Kasashe Takardar Zama ’Yan Najeriya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da ba wasu 'yan kasashen waje shaidar zama cikakkun 'yan Najeriya
  • Wannan ya faru ne a gidan gwamnati, inda shugaban ya bayyana abubuwan da yake sa ran jama'ar na waje za su bi
  • Gwamnatin Najeriya ta ce kasar na maraba da duk wasu 'yan wasu kasashe da za su kawo kasar ci gaba

FCT, Abuja - A Alhamis 15 ga watan Satumba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa mutum 286 'yan kasar waje takardar shaidan zama ‘yan Najeriya.

Rahoton Daily Trust ya ce, mutanen sun fito ne daga kasashen Birtaniya, Amurka, Siriya, Lebanon, Falasdinu, Masar da Italiya.

208 daga cikinsu an ba su takardar shaidar zama asalin ‘yan kasa yayin da sauran 78 kuma suka samu takardar shaidar zama dan Najeriya ta hanyar rajista.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

Buhari ya ba wasu 'yan kasar waje shaidar zama 'yan Najeriya
Buhari Ya Ba Amurkawa, ’Yan Birtaniya da Sauran Kasashe Takardar Zama ’Yan Najeriya | Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Buhari ya kuma yabawa ma’aikatar harkokin cikin gida da ta tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne suka samu takardun kamar yadda majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta ba da shawara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kun zama cikakkun 'yan Najeriya

Ya kuma tabbatar wa da wadannan sabbin 'yan Najeriya cewa, kasa ce mai cike da damammaki, daidaito da kuma ‘yanci kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada tare da taya su murna ikon zama da suka samu, rahoton Punch.

Buhari ya ce:

“Kun yi mubaya’arku ga Najeriya. Yayin da kuka ba Najeriya soyayyarku da amincinku, za saka muku da soyayyarta da amincinta.
“Ba tare da la'akari da inda kuka fito, ko wane addini kuke bi, kasar nan yanzu kasarku ce. Tarihinmu yanzu tarihin ku ne, al'adunmu ma yanzu al'adunku ne. Najeriya gidan ku ce, abin alfahari da farin cikinku."

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

Halazalika, Buhari ya nemi su kasance masu son Najeriya tare da bin duk wata doka, ka'ida da abin da kasar ke mutuntawa.

Karshe ya yi kira ga kananan hukumomi da su tabbatar da wadannan sabbin 'yan Najeriya sun samu cikakkiyar shaidar don more zama a inda suke rayuwa.

Buhari Ya Kori Dikio, Ya Nada Ndiomu a Matsayin Sabon Shugaban Shirin Yafiya Na Shugaban Kasa

A wani labarin, yanzu muke samun labarin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Barry Ndiomu (Mai Ritaya) a matsayin sabon mai kula da shirin yafiya na shugaban kasa (PAP).

Ndiomu dai zai maye gurbin tsohon mai kula da shirin ne Kanar Millan Dixon Dikio (mai ritaya) bisa umarnin Buhari, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wata sanarwa hadimin Buhari, Femi Adesina ya fitar ta ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada Manjo Janar Barry Tariye Ndiomu (mai ritaya) a matsayin shugaban rikon kwarya na shirin yafiya na shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Tashin hankali ga 'yan Najeriya yayin da Buhari yace zai haramta amfani da kananzir

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel