Gwamnatin Buhari Ta Hana Gidajen Rediyo Sanya Wakar ‘Warr’ da 'A Sosa' Na Ado Gwanjo

Gwamnatin Buhari Ta Hana Gidajen Rediyo Sanya Wakar ‘Warr’ da 'A Sosa' Na Ado Gwanjo

  • Hukumar Watsa Labarai ta kasa ta dira kan Ado Gwanja, ta haramtawa gidajen rediyo sanya wakarsa
  • A makwannin da suka gabata ne malamai da sauran jama'ar gari suka yi ta cece-kuce kan wakar Gwanja mai suna Warr
  • Ana yawan samun rikice-rikice da mawakan Hausa a Arewacin Najeriya bisa aron al'adun da basu dace ba

Kaduna - Makwannin da suka gabata ne kafafen sada zumunta a Arewacin Najeriya suka dauki dumi yayin da wani mawakin Hausa, Ado Gwanja ya saki wata waka mai cike da maganganun da suka saba al'ada.

Malamai da masu tsokaci sun yi ca kan wakokin 'Warr' da 'A Sosa', inda suka zargi Gwanjo da kawo wani sabon salon bata tarbiyya da kawo tsaiko ga al'adar Mallam Bahaushe.

Bayan cece-kuce da koke daga malamai da masu sharhin lamurran yau da kullum, gwamnati ta bayyana daukar mataki kan gidajen rediyo dake yada wakar.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

An hana saka wakar Warr ta Ado Gwanja
Gwamnatin Buhari Ta Hana Gidajen Rediyo Sanya Wakar ‘Warr’ da 'A Sosa' Na Ado Gwanjo | Hoto: Hassan Adamu Yusuf
Asali: UGC

A wata sanarwa da Hukumar Watsa Labarai ta Kasa (NBC) ta fitar, ya bayyana bukatar cewa, ya kamata gidajen rediyo suke kallon tsanaki kafin fara sanya wakoki a kafafensu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce, labari ya iso hukumar cewa, akwai gidajen rediyon dake sanya wakar 'Warr', don haka ta bukaci a dakata da hakan tare da gudun irin wadannan wakoki masu bata tarbiyya da kuma nuna alamar marisa daga buguwa.

A cewar hukumar, ci gaba da sanya wakar da makamanciyarta sun saba sashe na 3.18.1 (c) da 3.9 na kudin tsarin hukumar watsa labarai ta kasa.

Idan baku manta ba, a makon nan ne aka tashi da labarin cewa, hukumomi da daidaikun mutane sun maka Gwanja da wasu mawakan da ke irin wadannan wakokin a kotu, inda tuni aka mika musu sammaci.

Kano: An Yi Ƙarar Fitattun Mawakan Arewa Hip-Hop Mr 442, Safara'u, Gwanja Da Wasu Yan TikTok A Kotun Shari'a

Kara karanta wannan

Ambaliyar Ruwa: Ta Karewa Mayakan Boko Haram, Suna Fama Da Karancin Abinci Da Makamai

A wani labarin, an yi karar wasu mawakan gambara na arewa da masu fada a ji a TikTok a babban kotun shari'a da ke Bichi, Kano kan aikata abubuwan 'gurbata tarbiyya'.

Duk da cewa ba a samu ganin kwafin takardar karar da aka shigar ba, majiya da ke da masaniya kan lamarin ta shaida wa Daily Nigerian cewa laifin na da alaka da wakoki da bidiyon TikTok da ka iya lalata tarbiyar al'umma.

Amma Daily Nigerian ta samu kwafin wasikar da kotun shari'ar ta rubuta wa rundunar yan sanda inda ta bukaci ta yi bincike kan koken da mai shigar da karar ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.