Kano: An Yi Ƙarar Fitattun Mawakan Arewa Hip-Hop Mr 442, Safara'u, Gwanja Da Wasu Yan TikTok A Kotun Shari'a

Kano: An Yi Ƙarar Fitattun Mawakan Arewa Hip-Hop Mr 442, Safara'u, Gwanja Da Wasu Yan TikTok A Kotun Shari'a

  • An yi karar mawakan gambara na arewa irinsu Mista 442, Safara'u, Ado Gwanja da wasu 'yan TikTok a kotun shari'ar musulunci da ke Kano
  • Bayan shigar da karar kotun, Alkali ya rubuta wasika ga rundunar yan sandan Kano yana bukatar a yi bincike kan koken da aka shigar game da jaruman da mawakan
  • Wasikar da kotun ta rubuta wa kwamishinan yan sandan Kano ya nuna wasu lauyoyi tara ne suka shigar da karar suna zargin jaruman da bata tarbiyar al'umma

Jihar Kano - An yi karar wasu mawakan gambara na arewa da masu fada a ji a TikTok a babban kotun shari'a da ke Bichi, Kano kan aikata abubuwan 'gurbata tarbiyya'.

Duk da cewa ba a samu ganin kwafin takardar karar da aka shigar ba, majiya da ke da masaniya kan lamarin ta shaida wa Daily Nigerian cewa laifin na da alaka da wakoki da bidiyon TikTok da ka iya lalata tarbiyar al'umma.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

Mista 442 da Safara'u
Kano: An Yi Ƙarar Fitattun Mawakan Arewa Hip-Hop Mr 442, Safara'u, Gwanja Da Wasu Yan TikTok A Kotun Shari'a. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma Daily Nigerian ta samu kwafin wasikar da kotun shari'ar ta rubuta wa rundunar yan sanda inda ta bukaci ta yi bincike kan koken da mai shigar da karar ya yi.

Sunayen mawaka da fitattun masu fada a ji da aka yi kara a Kano

Wadanda abin ya shafa a cikin wasikar da aka aike wa kwamishinan yan sandan jihar Kano sune Mista 442, Safara'u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Ɗan Sarki, Ado Gwanja, Murja Kunya, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiyana.

Wasikar mai dauke da sa hannun rajistara na kotu, Aminu Muhd ta ce:

"Bayan korafin da Muhd Ali Hamza Esq, Abba Mahmud, Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B.I Usman Esq, Muhd Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi & Badamasi Suleiman Gandu Esq suka shigar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

"Alkalin babban kotun shari'a na Bichi, Kano ya umurci in rubuta takarda kuma in bukaci ka yi bincike kan wadanda ake zargi da aka ambata don daukan matakin da ya dace.
"Kwafin wasikar korafin yana tare da wannan domin ka duba.
"Kamar yadda aka saba, muna fatan samun hadin kai daga gare ka."

Takardar kotu
Kano: An Yi Ƙarar Fitattun Mawakan Arewa Hip-Hop Mr 442, Safara'u, Gwanja Da Wasu Yan TikTok A Kotun Shari'a. Hoto: Arewa Nahiya.
Asali: Facebook

Kannywood: Mafi Yawancin Mutane Za Su Saka Jaruman Fim A Wuta Idan Aka Ba Su Dama, In Ji Hauwa Waraka

A wani rahoton, Hauwa Abubakar, da aka fi sani da Hauwa Waraka a Kannywood, ta ce mutane da dama za su tsinduma jarumai a wuta idan suna da dama, Daily Trust ta rahoto.

Waraka, wacce ta bayyana hakan yayin hira da BBC a ranar Alhamis, ta nuna bacin rai kan zargi marasa kyau da mutane ke yi wa jarumai mata.

Jarumai fina-finan wacce aka haifa a Jos kuma ta girma a Kano, ta fuskanci zargin rashin da'a a masan'antar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel