Wasu ’Yan’uwa Biyu Sun Sare Hannun Mahaifinsu Don Su Sace Shanunsa

Wasu ’Yan’uwa Biyu Sun Sare Hannun Mahaifinsu Don Su Sace Shanunsa

  • Wasu 'yan uwa biyu sun datse hannun mahaifinsu saboda su sace shanunsa a wani yankin jihar Neja
  • Majiya ta bayyana cewa, 'ya'yan nasa sun hada baki da wasu domin su kora shanunsa, amma lamarin ya ci tura
  • An gurfanar da 'ya'yan biyu, kuma an shiga neman sauran mutanen da suka hada baki wajen laifin

Minna, jihar Neja - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wani wa da kani sun guntule hannun mahaifinsu dan shekara 60 don kawai su samu damar sace shanunsa.

'Yan uwan biyu da aka ce makiyaya ne, sune Bello Usman da Shehu Abubakar, kuma sun hada baki ne da wasu mutane biyu domin aikata wannan mummunan barna.

Hukumar binciken manyan laifuka ta kasa (SCIID) ta gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumarsa laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma aikata ta'addanci mai cutarwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu

Yadda 'ya'ya suka sare hannun mahaifinsu don su saci shanunsa
Wasu ’yan’uwa biyu sun sare hannun mahaifinsu don su sace shanunsa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shehu sa Bello, wadanda suka amsa aikata laifinsu, sun ce sun yi kokarin sace shanun mahaifin nasu ne amma ya kawo musu cikas, daga suka ce basu da zabnin da ya wuce su sare hannunsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ganin da manima labarai suka yi, sun ce an datse hannu daya na dattijon gaba dayansa yayin da dayan kuma ya kusa gutsurewa sai aka daure shi bandeji, BrainNews ta tattaro.

Sauran mutanen biyu da ake zargin sun aikata laifin tare sun tsere, sai dai an gayyato iyalansu, kuma an nemi su nemo su duk inda suka shiga nan da ranar da kotu za ta sake zama.

Alkalin kotun Minna, Fati Hassan Umar, ta ba da umarnin ci gaba da tsare tsagerun a hannun ‘yan sanda har zuwa ranar 26 ga watan Satumba.

Rahoton ya ce, an garzayo da dattijon ne kotu daga asibitin da yake jinya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan ta'adda suka farmaki yankin Kaduna, sun sace mutane, sun kashe wasu

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Karamar Hukuma, Henry Gotip a Jihar Filato

A wani labarin, yanzu muke samun labarin cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Henry Gotip da sanyin safiyar yau Laraba 7 ga watan Satumba.

Rahoto ya ce an sacea Gotip ne a gidansa dake Kwang a karamar hukumar Jos ta Arewa, rahoton jaridar This Day.

Majiya ta ce, an 'yan bindigan sun yi harbe-harbe don tsorata mazauna yankin kafin yin awon gaba da Gotip.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel