'Yan Ta’adda Sun Kashe ’Yan Wasu Uwa 2, Sun Yi Awon Gaba da 13 a Garin Kaduna

'Yan Ta’adda Sun Kashe ’Yan Wasu Uwa 2, Sun Yi Awon Gaba da 13 a Garin Kaduna

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki wani yankin jihar Kaduna, sun hallaka mutum biyu yayin da suka sace mutum 13
  • Wani malamin coci ya bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce wasu mutum hudu sun kubuta daga hannun tsagerun
  • Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna na ci gaba da bincike don sanar da al'umma halin da ake ciki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kaduna - A daren jiya Talata ne wasu gungun ‘yan ta’adda suka farmaki Katun Gida a unguwar Idon dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, sun kashe wa da kani tare da yin awon gaba da wasu mazauna garin 13.

Wani malamin addini Katun Gida da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa jaridar Leadership cewa, lamarin ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Satumba a Kaduna.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace shugaban karamar hukuma a jihar Arewa

A cewarsa, ‘yan bindigan sun zagaye kauyen ne da misalin karfe 11 na dare, inda suka fara harbe-harbe ba ji ba gani.

Yadda 'yan bindiga sun sace mutum 13, sun hallaka mutum 2
'Yan Ta’adda Sun Kashe ’Yan Wasu Uwa 2, Sun Yi Awon Gaba da 13 a Garin Kaduna | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Da misalin karfe 11 zuwa 12 na daren ranar Talata, an farmaki daya daga cikin majami’ata a Katun Gida, an kashe ‘yan uwana har biyu a harin.
An sace mutum 13, a yawansu mambobin coci na ne. Mutum 3 daga cikin 13 da aka sace sun kubuta, 'yan bindigan sun kuma sako wani mutumin da matarsa bata da lafiya domin ya kai ta asibiti.
"Har yanzu sauran mutum takwas din ta hannun ‘yan bindigan. Muna da kusan mutum hudu da aka sace daga gida daya."

Ya kuma bayyana sunayen wadanda aka kashen da Bulu Yohanna da Silas Yohanna.

Daga karshe ya yi addu'ar Allah ya bayyana su.

Jaridar ta kira mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige, ya ce zai tabbatar kafin yin bayani ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Mutum 43 Da Aka Sace A Masallacin A Zamfara Sun Samu Kubuta Bayan Biya Kudi, Daya Ya Mutu

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Karamar Hukuma, Henry Gotip a Jihar Filato

A wani labarin, yanzu muke samun labarin cewa, wasu tsagerun ‘yan bindiga yi awon gaba da shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Henry Gotip da sanyin safiyar yau Laraba 7 ga watan Satumba.

Rahoto ya ce an sacea Gotip ne a gidansa dake Kwang a karamar hukumar Jos ta Arewa, rahoton jaridar This Day.

Majiya ta ce, an 'yan bindigan sun yi harbe-harbe don tsorata mazauna yankin kafin yin awon gaba da Gotip.

Asali: Legit.ng

Online view pixel