Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Dira Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu

Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Dira Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu

  • Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya sun dira gidan Malam Tukur Mamu dake Kaduna tare da bincike shi tsaf
  • Kamar yadda ganau ya bayyana, jami'an sun bayyana a motoci kusan 20 kuma sun kwashe takardu, wayoyi da kwamfuyutoci
  • A sa'o'in farko na ranar Alhamis suka dira gidan inda daga nan suka zarce ofishinsa domin cigaba da bincike

Kaduna - Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun kutsa gidan Tukur Mamu, mai sasanci tsakanin 'yan bindiga da iyalan wadanda suka sace a Kaduna a sa'o'in farko na ranar Alhamis.

Da Dumi
Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu
Asali: Original

Jami'an sun bayyana a kusan motoci 20 wanda ganau ne ya tabbatar da hakan ga Daily Trust.

"Sun bincike gidan tare da yin awon gaba da takardu, wayoyi da kwamfuyutoci."

- Ganau ya tabbatar da hakan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Yadda Hannu a Karbar Kudin Fansa har N2b da Alaka da Kungiyar Ta'addanci ta sa aka Kama Mamu

Daily Trust ta tattaro cewa, bayan kai samamen gidansa, sun kara da zuwa ofishinsa dake Kaduna.

Fasinjojin da suka samu 'yanci daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna su kan tattaru a ofishin mamu kafin su sadu da 'yan uwansu.

Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa an kama Mame kan zarginsa da hannu wurin karbar kudin fansa da kai wa 'yan ta'adda domin sakin wadanda suka sace.

Karin bayani nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel