Hotuna Da Bidiyoyi: Ooni Na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, Ya Yi Sabuwar Amarya Ajin Farko

Hotuna Da Bidiyoyi: Ooni Na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, Ya Yi Sabuwar Amarya Ajin Farko

  • Watanni bayan rabuwarsa da tsohuwar matarsa, mai martaba Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, ya yi sabuwar amarya
  • Basaraken ya yi wuff da kyakkyawar budurwa mai suna Olori Mariam Anako a wani kasaitaccen biki da aka gudanar
  • Bidiyoyi da hotunan shagalin bikin sun yadu a shafukan soshiyal midiya bayan hadimin sarkin, Moses Olafare, ya sake su

Jihar Osun - Babban basaraken kasar Yarbawa mai daraja ta daya, Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi ya angwance da wata kyakyawar budurwa.

Hakan na zuwa ne yan watanni bayan ana ta yada jita-jitan cewa basaraken na shirye-shiryen yin sabuwar amarya.

Ooni na Ife da sabuwar amaryarsa
Hotuna Da Bidiyoyi: Ooni Na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, Ya Yi Sabuwar Amarya Ajin Farko Hoto: lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Shafin LIB ya rahoto cewa daraktan labarai na mai martaba Ooni, Moses Olafare ne ya yada hotunan bikin a shafukan soshiyal midiya.

Sunan sabuwar amaryar Olori Mariam Anako kuma an tattaro cewa tun a watan Maris aka fara shirye-shiryen auren. A wannan lokacin ne basaraken ya aika manyan tawaga zuwa gidan amaryar domin su nema masa aurenta.

Kara karanta wannan

Mun gane kuskurenmu: Wasu ‘Yan daban Siyasa Sun Ajiye Makamai, Sun Shiga APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon auren nasa na zuwa ne watanni 10 bayan amaryarsa, Naomi Silekunola, ta rabu da sarkin.

Kafin nada shi sarki, Ooni ya auri Adebukola Bombata a 2008 amma suka rabu. Bayan nada shi, ya auri haifaffiyar yar jihar Edo Zaynab-Otiti Obanor a 2016 amma watanni 17 kawai suka yi tare sannan suka rabu.

Daga nan sai Ooni ya auri Silekunola a 2018 har suka haifi yaro daya tare kafin rabuwarsu a watan Disamba.

Kalli hotuna da bidiyoyin bikin a kasa:

Hotunan Ado Gwanja Da Momee Gombe Sun Haddasa Cece-kuce A Soshiyal Midiya

A wani labari na daban, jama’a sun shiga rudani bayan bayyanar wasu hotuna na manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ado Gwanja da Momee Gombe a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

A cikin hotunan wadanda tuni suka yadu a shafukan sadarwa, an gano jaruman biyu cikin shiga da ta fi kama da ta sabbin ma'aurata kuma sun yi tsayuwar daukar hoto sak irin na amarya da ango.

Wannan al’amari ya jefa mutane cikin shakku, yayin da wasu ke ganin shirin fim ne, wasu kuma sun yi fatan Allah yasa hakan ya zamo gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel