Shugaban Kasa Ya Ba Dakaru Wa’adi Domin Ganin Karshen ‘Yan ta’dda da ‘Yan Bindiga

Shugaban Kasa Ya Ba Dakaru Wa’adi Domin Ganin Karshen ‘Yan ta’dda da ‘Yan Bindiga

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci hafsoshin tsaro su ga bayan duk wasu masu tada kayar baya a kasar nan
  • Rauf Ogbeni Aregbesola ya sanar da wannan da ya kira taron manema labarai, aka yi magana game da batun tsaro
  • Ministan harkokin gidan yace an ba jami’an tsaro wa’adi zuwa Disamba a ga karshen ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A farkon makon nan, Mai girma Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasa su magance duk wata matsalar rashin tsaro a fadin Najeriya.

This Day tace Shugaban kasar ya bada wannan umarni ne ta bakin Alhaji Rauf Ogbeni Aregbesola, wanda shi ne Ministan harkokin cikin gida na tarayya.

Rauf Ogbeni Aregbesola ya kira taron manema labarai, sun yi masu jawabi a birnin tarayya Abuja.

A wajen wannan tattaunawa, an maida hankali a kan abin da ya shafi irin kokarin da gwamnatin Muhammau Buhari take yi wajen kawo zaman lafiya a yau.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Tace Ta Magance Mafi Munin Matsalar Tsaro a Najeriya

Ministocin yada labarai da na tsaro da harkokin ‘yan sanda; Lai Mohammed, Janar Bashir Magashi da Mohammed Dingyadi sun tofa albarkacin bakinsu.

Daga yanzu zuwa Disamba mai zuwa

A wajen taron ne aka rahoto Aregbesola yana cewa shugaban kasa ya ba hafsoshin tsaro umarni suyi kokarin kawo karshen ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Kasa
MUHAMMADU BUHARI ya kaddamar da shirin National Crisis Management Doctrine Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Duba da halin da ake ciki, Mai girma Muhammadu Buhari yana so a magance duk wasu matsalolin rashin tsaro da kashe-kashe zuwa karshen shekarar nan.

An fara samun sauki - Ministoci

Bashir Magashi ya yi bayanin yadda jami’an tsaro suka tsare hanyar Abuja-Kaduna, wanda kafin yanzu ‘yan bindiga suke tare mutane, suna yin garkuwa da su.

Ministan tsaron ya tabbatar da cewa sojoji da jami’an tsaro suna bakin kokarins domin kawo karshen kashe-kashe a Arewa da satar mai a Kudu maso kudu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

A cewar Alhaji Dingyadi, an fara samun zaman lafiya a hanyoyi kamar na Abuja-Kaduna, Kaduna-Birnin-Gwari, Sokoto-Zamfara, da titin Zamfara-Kaduna.

Shugaban Najeriya ya dade yana nuna yadda ya damu da halin rashin tsaro da al’umma ke ciki.

Legit.ng Hausa ta fahimci ba wannan ne karon farko da gwamnatin tarayya ta bada irin wannan wa’adi ba, an yi haka a 2015 wajen yaki da 'Yan Boko Haram.

'Yan bangar siyasa sun zama 'Yan APC

Bayan shekara da shekaru su na ta'adi, kun samu labari Baba Karami da Garba Lawal sun tuba, sun ce yanzu sun gano ‘yan siyasa sun rika amfani da su ne.

Baba Karami da Garba Lawal sun shiga APC, kuma an yi wa tubabbun tsagerun alkawarin sun zama ‘yan halal a APC, muddin ba su koma gidan jiya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel