Kawo Yanzu, Mutum 60 Sun Rasa Rayukansu A Jigawa Sakamakon Ambaliya

Kawo Yanzu, Mutum 60 Sun Rasa Rayukansu A Jigawa Sakamakon Ambaliya

  • Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan sama a jihar Jigawa ya karu makon nan
  • Shugaban hukumar SEMA yace har yanzu gwamnatin jihar bata basu ko sisi ba don taimakawa mutane
  • Hukumar hasashen yanayin Najeriya NiMet ta bayyana cewa wasu jihohin Najeriya zasu fuskanci ambaliya

Dutse - Hukumar bada agaji ta jihar Jigawa SEMA ta bayyana cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan sama ya kai 60.

Ta kara da cewa tuni an kafa sansanin yan gudun hijra 11 a fadin jihar don kula da wadanda suka rasa muhallansu.

Sakataren hukumar, Alhaji Yusuf Sani Babura, ya bayyana hakan a hira da manema labarai hakan a Dutse, babbar birnin jihar, rahoton TheNation.

Yace:

"Kawo makon da ya gabata, mutum 50 aka tabbatar sun mutu. Wannan makon, an tabbatar da mutuwar mutum shida; yanzu jimillar mutum 56 ne suka mutu sakamakon ambaliya."

"Bayan haka na samu labarin cewa wani jirgin ruwa ya kife kuma mutum hudu sun mutu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce hukumar ya bude sansanin yan gudun hijra 11 a Hadejia, biyu a Miga, biyu a Dutse da kuma daya a BirninKudu.

Flood
Kawo Yanzu, Mutum 60 Sun Rasa Rayukansu A Jigawa Sakamakon Ambaliya
Asali: Original

Babura yace duk da kudin bashi suke wadannan ayyuka saboda har yanzu gwamnatin jihar bata basu ko sisi ba.

A baya kun ji cewa sama da mutum 2,051 sun rasa muhallasu sakamakon ruwan saman da akayi ranar Lahadi.

Sauran garuruwan da abin ya shafa sune Sankara, da Gwaram.

Mutane Guda 15 Sun Nutse A Rafi A Borno, An Ciro Gawarwaki

A wani labarin kuwa, akalla gawarwaki guda 15 ne aka ciro daga Rafin Ngadabul da yayi ambaliya a Maiduguri, Jihar Borno, The Punch ta rahoto.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na kasa NEMA na yankin arewa maso gabas, Mohammed Usman ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba yayin hira da NAN a Maiduguri.

Usman ya ce ana samun karuwar mutane da ke nutsewa a rafin da ya yi ambaliya a garuruwan da ke gabar rafin a Maiduguri.

Ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara su rika yi wa yaransu gargadi su dena zuwa wanka a rafin don gudun nutsewa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel