Yadda Matashi Ya Doke Mahaifansa Da Tabarya Har Lahira A Jigawa, An Cafke Shi

Yadda Matashi Ya Doke Mahaifansa Da Tabarya Har Lahira A Jigawa, An Cafke Shi

  • Wani matashi dan shekaru 37 ya kashe iyayensa a karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa
  • Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta ce Munkaila Ahmadu ya yi amfani da tabarya wajen doke mahaifiyarsa da mahaifinsa inda suka kwanta dama
  • Munkaila ya kuma jikkata wasu mazauna yankin guda biyu wadanda a yanzu haka suna asibiti a kwance

Jigawa - Wani matashi dan shekara 37 mai suna Munkaila Ahmadu, ya halaka mahaifansa a kauyen Zarada-Sabuwa da ke karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya saki.

Adam ya ce Munkaila ya yi amfani da tabarya wajen doke mahaifinsa, Ahmad Muhammad mai shekaru 70 wanda shine hakimin kauyen da kuma mahaifiyar Hauwa Ahmadu mai shekaru 60.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani kasurgumin dillalin bindiga dauke da makamai zai tafi Zamfara

Yan sanda
Yadda Matashi Ya Doke Mahaifansa Da Tabarya Har Lahira A Jigawa, An Cafke Shi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Daily Trust ta kuma rahoto cewa matashin ya farmaki wasu mazauna yankin biyu, Kailu Badugu mai shekaru 65 da kuma Hakalima Amadu mai shekaru 50.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin yan sandan ya ce:

“Da samun rahoton wannan mummunan al’amari, wata tawagar jami’an yan sanda sun ziyarci wajen da aka aikata laifin sannan suka kwashe wadanda abun ya ritsa da su zuwa babban asibitin Gumel.
“Likita ya tabbatar da mutuwar Ahmadu Muhammad da Hauwa Ahmadu sakamakon raunin da suka ji a kansu yayin da aka kwantar da Kailu Badugu da Hakalima Ahmadu wadanda suka ji rauni daban-daban.”

Kakakin yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin sannan an kwato makamin.

Ya kara da cewa:

“Binciken farko ya nuna cewa Ahmad Muhammad da Hauwa Ahmadu sune suka haifi wanda ake zargin a cikinsu.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida, ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse, domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da mai laifin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dalibai Da Jami'an Tsaron Adamu Sun Yi Arangama A Hedkwatar APC A Abuja

Bacin Rana: Matar Aure Ta Fallawa Mai Wasan Barkwanci Mari Bayan Ya Nemi Su Sha Soyayya A Bidiyo

A wani labari na daban, wata matar aure ta fusata bayan wani matashi ya isa gareta sannan ya nemi soyayyarta. A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, mutumin mai suna Deehans ya tunkari matar sannan ya nemi ta bashi lambar wayarta.

Cikin mutunci ta ki amsa bukatar shi sannan ta sanar da shi cewa tana da aure. Sai dai kuma, wannan amsa tata bai sa matashin ya halura ba inda ya nemi su kebe su sha soyayya.

Wannan ya tunzura kyakkyawar matar, inda ta wanka masa lafiyayyen mari. Bayan nan sai ta tsaya a bakin kofar sannan ta ja hankalin mijinta, nan take ya fito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel