Barayin Mai: Gwamnati Ta Kawo Hujjar Ba Tsohon Tsageran N/Delta Kwangilar N48bn

Barayin Mai: Gwamnati Ta Kawo Hujjar Ba Tsohon Tsageran N/Delta Kwangilar N48bn

  • A lokacin da Najeriya take takama da sojojin sama da na ruwa da na kasa, sai aka ji an ba su Government Ekpemupolo kwangila
  • Kamfaninsu Government Ekpemupolo watau Tompolo aka ba kwangilar bada kariya ga duk wasu bututun mai na Neje Delta
  • Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari yace sun bada aikin ne domin akwai bukatar a kawo karshen satar mai da ake tayi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta fito tana cewa ta dauki matakin da ya kamata wajen bada kwangilar bada kariya ga bututun mai ga Government Ekpemupolo.

A ranar Talata, shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari ya wanke gwamnati daga zargin masu zargi. Jaridar The Cable ce ta fitar da wannan rahoton a jiya.

Kyari ya zanta da manema labarai a fadar shugaban kasa a Abuja, yace bukata ce ta jawo kamfanin NNPC ya bada aikin nan ga su Government Ekpemupolo.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Osinbajo ya shiga batun ASUU, ya fadi abin da gwamnati za ta yi

Kamar dai yadda aka sani, Ekpemupolo mai shekara 51, tsohon tsagera ne a yankin Neja-Delta, ya taba rike shugabancin kungiyar tsageru na MEND a baya.

NNPC: Mun yi abin da ya kamata

Ganin yadda aka damka amanar arzikin man Najeriya ga wannan mutumi ya sa wasu suke sukar lamarin, amma Mele Kolo Kyari yace hakan shi ne daidai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Punch ta rahoto shugaban NNPC yana cewa gwamnati na bukatar ta bada kwangilar tsare bututun ga kamfanoni masu zaman kansu saboda satar da ake yi.

Kyari ya shaidawa manema labarai cewa ba wannan ne karon farko da mutanen Neja-Delta suka samu kwangila irin wannan ba, yace an yi irin haka a baya.

Barayin Mai
Bututun mai a Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Bukata ce ta tashi - NNPC

“Muna bukatar ‘yan kasuwa su kula da bututun nan. Saboda haka sai muka kira ‘yan kwangila su nemi aikin.

Kara karanta wannan

Babban Magana: Masallatai Da Coci-Coci Suna Satar Ɗanyen Man Fetur A Najeriya, In Ji Shugaban NNPC, Kyari

Kuma aka bi ka’ida, aka kai ga zaben wanda ya ci kwangila. Nayi imani cewa mun yi abin da ya kamata."
“Ba kowa zai iya wannan aiki ba, kuma ana ambaton Tompolo ne kawai. Da kamfanoni muke aiki.
Watakila yana da hannu a kamfanin, amma ba da Government Ekpemupolo (Tompolo) muke aiki ba.

Tompolo zai ja kaya shi kadai

The Nation tace an ba Tompolo aikin tsare arzikin kasar ne a kan Naira biliyan hudu duk wata, a karshen shekara zai tashi da Naira biliyan 48 daga kwangilar.

Wasu tsageru da kungiyoyin ta’adda sun ji haushin yadda aka ba Tompolo wannan kwangila mai tsoka shi kadai, suka sha alwashin kawowa aikin tasgaro.

Ra'ayin Gwamnonin jihohi

Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa ya fitar da jawabi ta bakin Olisa Ifeajika, yana yabon gwamnati a kan matakin da ta dauka na ba kamfanin Tompolo wannan aiki.

Amma Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo yana ganin bai dace a dauki kwangilar tsaron dukiya irin wannan, a damkawa wasu daidaikun mutane ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zai siyar da kamfanin man fetur idan ya gaji Buahri, ya fadi wadanda za su siya

Asali: Legit.ng

Online view pixel