Masallatai Da Coci-Coci Suna Satar Danyen Man Fetur A Najeriya, In Ji Shugaban NNPC, Kyari

Masallatai Da Coci-Coci Suna Satar Danyen Man Fetur A Najeriya, In Ji Shugaban NNPC, Kyari

  • Mista Mele Kyari shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya yi zargin cewa masallatai da coci-coci da suna da hannu wurin satar danyen man fetur
  • Kyari ya ce bayan wata gobara da bututun mai ta yi, binciken da aka yi ya nuna wasu mutane sun ja bututun mai gidajensu suna sace mai kuma an gano cikin masu satar da har masallatai da coci
  • Shugaban na NNPC yaa kuma ce nan da tsakiyar shekarar 2023 Najeriya za ta dena siyo mai daga kasashen waje domin matatan Dangote da sauran matatun Najeriya za su fara aiki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Kamfanin Man Fetur Na Najeriya, NNPC, ta zargi jami'an gwamnati, malaman addini, hukumomin tsaro da ma wasu ma'aikatanta da hannu wurin satar danyen mai a kasar, The Punch ta rahoto.

Da ya ke magana a wurin taron tawagar shugaban kasa karo na 49 a gidan gwamnati a Abuja, Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce dukkan rukunin mutanen kasar na da hannu a laifin.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC Ya Sanar Da Lokacin Da Najeriya Za Ta Dena Siyo Mai Daga Kasashen Waje

Mele Kyari II
Babban Magana: An Gano Danyen Man Fetur Na Sata A Masallatai Da Coci, Mele Kyari. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa duk lokacin da aka samu kayan matar a masallatai da coci-coci, akwai wasu masu barnata kayan gwamnati da ke aiki da su.

Kyari ya ce:

"A lokacin da aka samu gobara daya cikin bututun mu, mun gano bututun ta shiga gidajen wasu mutane. Bayan haka, duk da nuna cewa mu masu addini ne, ka san cewa wasu daga cikin bututun da danyen man mun gano su a coci-coci ne da masallatai.
"Hakan na nufin kowa na aikata laifin. Babu yadda za a yi ka kwaso kaya ka loda a motocci zuwa unguwanni da akwai mutane da dama ba tare da wani ya ganka ba. Kowa har da mutanen unguwa, malaman addini da kuma wata kila jami'an gwamnati, ciki har da jami'an tsaro.
"Suna nan ko ina. Na ga hakan har a Neja Delta. Babu yadda za a yi ka tura abu ka rasa kashi 30 cikin 100 sannan ka cigaba da tura kayan ta wannan bututun."

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zai siyar da kamfanin man fetur idan ya gaji Buahri, ya fadi wadanda za su siya

Za a kafa kamfani da za ta rika kula da bututun man fetur - Kyari

Saboda wannan dalilin, shugaban na NNPC ya ce an rufe dukkan bututun man fetur na kasar da ake tura mai saboda masu fasa bututun suna sata, Channels TV ta rahoto.

Ya kara da cewa za a kafa wata kamfani da za ta rika kula da bututun man fetur din don tabbatar ana rarraba man fetur a sassan kasar ba tare da ana sacewa ba.

Ya bada tabbacin cewa idan aka rungumi amfani da iskar gas, za a warware matsalar makamashi a kasar.

Shugaban NNPC Ya Sanar Da Lokacin Da Najeriya Za Ta Dena Siyo Mai Daga Kasashen Waje

A bangare guda, Shugaban kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya ce Najeriya za ta dena siyo man fetur daga kasashen waje lokacin da matatar Dangote ta fara aiki zuwa tsakiyar shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wurin taron da tawagar sadarwa ta shugaban kasa ta shirya karo na 49 a Villa, Abuja, The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel