Karin bayani a kan Abin da ya Hana Kotu ta Bada Abba Kyari a Damka shi ga Amurka

Karin bayani a kan Abin da ya Hana Kotu ta Bada Abba Kyari a Damka shi ga Amurka

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ta nemi kotu ta bada dama a sallama Abba Kyari domin ayi shari’a da shi a kotun Amurka
  • Alkalin kotun tarayya bai bada izinin hakan ba, yace babu yadda za ayi a saki Kyari a lokacin da ake shari’ar da shi a Najeriya
  • Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi mamakin yadda AGF ya shigar da wannan kara duk da shi ya ba NDLEA damar kai Kyari kotu

Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a Abuja ya ki amincewa da rokon da ake yi na mika Abba Kyari ga hukumomin Amurka domin ayi shari’a da shi.

Vanguard ta bi diddikin hukuncin da Mai shari’a Inyang Ekwo ya gabatar a ranar Litinin a Abuja, ta kawo rahoto kan abin da ya sa aka yi watsi da karar.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: Dan a mutun Kwankwaso ya rasa kujerar shugabancin PDP a Kano

Gwamnatin tarayya ta nemi izinin mika DCP Kyari ga kasar Amurka domin amsa tuhumar da ake yi masa na hannu a badakalar Ramon Abbas (Hushpuppi).

Alkali Ekwo yace karar da aka shigar ta ofishin Ministan shari’a, Abubakar Malami bai da karfi, kuma sam bai gamsar da kotu wajen samun wannan bukata ba.

Alkalin da ya saurari wannan kara a kotun tarayya, yace ya kamata Abubakar Malami SAN a matsayinsa na Ministan shari’a ya san abin da doka ta fada.

Abin da doka ta tanada

Mai shari’a Ekwo yace dokar sallama wanda ake zargi da laifi ba ta halatta a mikawa wata kasar waje mutumin da wata kotu take zargi da laifi a Najeriya ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abba Kyari
DCP Abba Kyari a Majalisar Tarayya Hoto: orderpaper.ng
Asali: UGC

A yanzu da ake neman a damka ‘dan sandan a hannun Amurka, hukumar NDLEA tana shari’a da shi a kotu kan zarginsa da laifin hannu a harkar kwayoyi.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kotun daukaka kara ta mayarwa wani dan takarar gwamnan PDP tikitinsa

Jaridar ta rahoto Ekwo yana mamakin yadda babban lauyan gwamnatin zai dumfari kotu da nufin a saki Kyari, alhali shi ya ba NDLEA damar ta kai shi kotu.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi mamaki

“AGF ba zai ce bai san da karar da aka shigar a kan wanda ake tuhuma (DCP Abba Kyari) ba, wanda hukumar NDLEA ta maka shi.
Doka tayi bayani karara, tun da an gurfanar da Kyari a gaban kotu mai aiki a Najeriya, ba za a mika shi ga kowa ba sai an gama shari’a.”

A dalilin wannan doka, babu yadda Alkali zai saurari kara mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022, sai lokacin da aka wanke Kyari ko aka kama shi da laifi.

REC: Za a sabawa dokar zabe

Kun ji labari sashe na 156(1)(a) na kundin tsarin mulkin ya haramta a dauki ‘Dan siyasa da yake da Jam’iyya, a ba shi mukami a karkashin Hukumar INEC.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Babbar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Bukatar Tasa Keyar Abba Kyari Zuwa Amurka

Sai ga shi kuma an ji labari shugaban kasa ya zabi ‘Dan takaran APC da wasu na kusa da Gwamnonin APC, a nada su a matsayin Kwamishinonin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel