Sunayen ‘Yan Siyasa da Bara-Gurbi da Buhari Ya Nemi Ya Cusa a INEC Sun Fito Fili

Sunayen ‘Yan Siyasa da Bara-Gurbi da Buhari Ya Nemi Ya Cusa a INEC Sun Fito Fili

  • An taso Muhammadu Buhari a gaba a game da nadin manyan Kwamishinoni na REC da yake shirin yi a hukumar INEC
  • Ana zargin shugaban kasar ya gabatar da sunayen wadanda suke siyasa da marasa gaskiya domin zama Kwamishinonin zabe
  • Dokar Najeriya ba ta hallatawa duk wani ‘dan jam’iyyar siyasa rike mukamanin REC a hukumar da ke gudanar da zabe ba

FCT, Abuja – A makon da ya gabata Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar dattawan Najeriya sunayen wadanda za a ba mukaman REC a INEC.

Legit.ng ta fahimci wannan takarda tana kunshe da sunayen mutane 19 da shugaban kasa ya zaba.

A cikin wadanda aka zakulo, mutum biyar za su koma kan kujerunsu ne idan an amince da nadinsu, yayin da ragowar za su dare kujerar a karon farko.

Sunayen 'yan karon farko

Kara karanta wannan

‘Dan gwagwarmaya Ya Fadawa Atiku, Obi da Kwankwaso Hanyar Doke Tinubu a Saukake

Ga wadanda aka zaba nan da kuma jihohin da suka fito:

Pauline Onyeka Ugochi (Imo)

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Farfesa Muhammad Lawal Bashir (Sokoto)

Farfesa Prof. Ayobami Salami (Oyo)

Zango Abdu (Katsina)

Queen Elizabeth Agwu (Ebonyi)

Agundu Tersoo (Benue)

Yomere Oritsemlebi (Delta)

Farfesa Yahaya Ibrahim (Kaduna)

Dr. Nura Ali (Kano)

Agu Uchenna Sylvia (Enugu).

Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: @BuhariSallau
Asali: Facebook

Inda matsalar take a jerin sunayen

Rahoto ya nuna cewa a cikin wadannan mutane da aka zaba, akwai wadanda ba su mukami a INEC ya saba domin ‘yan siyasa ne ko kuma sun taba aikata laifi.

Sashe na 156(1)(a) na kundin tsarin mulkin 1999 bai amincewa ‘dan siyasa ya zama kwamishina a INEC ba, amma a jerin da aka fitar, akwai wasu ‘ya ‘yan APC.

1. Farfesa Muhammad Lawal Bashir

Legit.ng ta fahimci Muhammad Lawal Bashir Farfesan tattalin arziki ne daga Sokoto, amma har takarar kujerar Gwamna ya yi a karkashin APC a zaben 2015.

Kara karanta wannan

Hotunan Mayakan Kasar Waje Masu Alaka Da Boko Haram Da Aka Kama A Benue

Farfesa Lawal Bashir yana cikin tsofaffin ‘ya ‘yan jam’iyyar CPC da ta narke a APC. Malamin jami'ar ya rasa tikiti ne a hannun Aminu Tambuwal a 2014.

2. Sylvia Uchenna Agu

Bincikenmu ya nuna mana Sylvia Uchenna Agu malama ce a jami’ar tarayya ta Nsukka, tun 19998 take koyarwa a sashen shugabanci da kananan hukumomi.

Sai dai ana zargin Sylvia Uchenna Agu ‘yaruwar mataimakin shugaban APC ne na yankin Kudu maso gabas, Emma Eneukwu wanda ya fito daga jihar Enugu.

3. Pauline Onyeka Ugochi

Wanda aka zaba daga jihar Imo ita ce Pauline Onyeka Ugochi. Ana zargin da hannunta aka rika murde zabe a lokacin ta na shugabar sashen ICT ta INEC a Imo.

Daga baya Gwamna Hope Uzodinma ya zabe ta a matsayin shugabar ISIEC ta jiha.

4. Queen Elizabeth Agwu

Ita kuwa Queen Elizabeth Agwu ta rike Akanta Janar a jihar Ebonyi, amma aka dakatar da ita daga ofis a 2016 saboda zargin rashin gaskiya da rashin sanin aiki.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Queen Elizabeth Agwu ta rike shugaban ma'aikatan fadar gwamnan Ebonyi. Kafin nan mun fahimci ta zama sakataren din-din-din a hukumar UBEB ta jihar.

Sauya-shekar Shekarau

Kun ji labarin yadda Ubrahim Shekarau ya fara siyasa a ANPP, daga baya ta dunkule a jam’iyyar da ta zama APC, a shekarar 2014 ya fice daga APC da suka kafa.

Daga 2015 zuwa yanzu, Malam Shekarau ya yi zama a PDP, ya koma APC kafin ya shiga NNPP, yanzu dai ya sake tsallakowa tafiyar PDP a shirin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng